
Kasashen Duniya







A ranar Alhamis aka zaɓi Ba'amurke Prevost a matsayin sabon Fafaroma Leo XIV. Rahoto ya nuna cewa an haifi Robert Prevost a Chicago a ranar 14 ga Satumba, 1955.

Bill Gates zai ba da kyautar dukiyarsa tare da rufe gidauniyar BMGF a 2045. Ya ce zai sadaukar da dukiyarsa gaba daya domin ceton rayuka da kuma inganta su a duniya.

Daya karshe bayan jimamin mutuwar Fafaroma Francis a ƙarshen watan Afrilu, an zabi sabon shugaban katolika Robert Francis Prevost wanda ya fito daga kasar Amurka.

Bill Gates ya zargi Elon Musk da kashe yaran talakawa a fadin duniya ta hanyar dakatar da ayyukan hukumar USAID. Gates ya ce zai rufe gidauniyarsa a 2045.

Isra'ila ta yi barazanar kai hari Iran kamar yadda ta yi wa Hamas da Hezbollah, bayan harin Houthi, kuma ta ce za ta iya kare kanta ba tare da taimakon Amurka ba.

Za a karrama wasu shugabannin Najeriya a birnin London. Za a karrama gwamna Umaru Bago, Seyi Tinubu, gwamnan Legas, ministan harkokin cikin gidan Najeriya.

Atiku Abubakar ya soki Bola Tinubu kan manufar kishin kasa, ya ce ya sayar da Escalade ya koma Innoson, kuma ya daina duba lafiya a ƙasashen waje.

Indiya ta kai hari Pakistan yayin da Pakistan ta ce ta harbo jiragen yaƙi 5. Indiya ta ce ta kai harin ne kan 'yan ta'adda, ikirarin da Pakistan ta karyata.

Isra'ila ta bayyana kokarin da take na kashe gobarar da ta tashi a bayan shafe sa'o'i 30 ba tare da kammala kashe gobarar ba. An kama wasu mutane kan tashin wutar.
Kasashen Duniya
Samu kari