
Jihar Benue







Rundunar tsaro a Najeriya ta ce makiyayan kasashen ketare ne ke kai hari a jihohin Benue da Plateau, inda suka shigowa ƙasar ta iyakoki masu rauni.

Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Benue. 'Yan bindigan sun hallaka wani basarake lokacin da yake aiki a gonarsa.

Majiyoyi sun ce wasu yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe wani jami’in ‘yan sanda da wani mutum a kauyen Ikyac-Gev da ke Makurdi a jihar Benue.

'Yan bindiga sun kashe jigon APC da wasu mutum uku a Benue a wani harin kwantan bauna da suka kai garuruwa biyu. An ce wannan ne hari na biyu a cikin makonni biyu.

Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana cewa akwai wani shiri da ake kullawa domin raba shi da kujerarsa. Ya ce masu wannan shirin ba za su yi nasara ba.

Lauyoyi sun nemi majalisar tarayya ta kwace ikon majalisun Benue da Zamfara saboda dakatar da 'yan majalisu 23. Sun hango abin da zai faru idan ba a dauki mataki ba.

Yayin da kashe-kashe ya yi yawa a Benue, Majalisar Wakilai ta zargi Gwamna Alia da watsi da dokar hana kiwo a fili, wanda ke haddasa rashin tsaro a jihar.

Rikicin iyaka da na al’umma ya kashe mutane 1,796 a Najeriya tun daga 2018 zuwa shekarar 2025, wanda kungiyar PIND ta tattaro bayanansu a jihoh da dama.

Rahotanni daga jihar Benue sun tabbatar da cewa jami'an tsaro sun kashe Aungwa Sesugh, wanda aka fi sani da Tino Brown, a harin Zaki-Biam da ke jihar Benue.
Jihar Benue
Samu kari