
Siyasar Najeriya







Peter Obi ya wanke kan shi daga zargin da aka masa kan cewa ya hada kai da Janar Sani Abacha wajen yin badakala. Obi ya ce kasuwanci ne ya hada su da Abacha.

Kungiyar magoya bayan APC a Arewacin Najeriya suj bayyana Mohammad Kailani a matsayin wanda ya dace ya karɓi shugabancin jam'iyya a matakin ƙasa.

An yi taron hadakar 'yan adawa karkashin ADC a jihar Gombe. 'Yan siyasa a PDP da APC sun shiga tafiyar hadaka a yayin taron da ADC ta ce ta shirya kayar da APC.

Ƴan takarar gwamna 2 a Ondo, Eyitayo Jegede, Agboola Ajayi da wasu jiga-jigan PDP sun koma ADC, inda suka shiga haɗakarsu Atiku domin kalubalantar APC a zaɓen 2027.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya yi magana kan batun zaben shekarar 2027 da ake yi. Ya bayyana cewa surutun da ake yi kan zaben bai dame shi ba.

Hadimin tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje mai suna Aminu Dahiru Ahmad ya ce za su rama abin da Bola Ahmed Tinubu ya musu a APC a jihar Kano.

Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Umar Iliya Damagum ya aika da sakon gargadi ga masu yi wa PDP zagon kasa. Ya ce za su dauki matakin ladabtarwa.

Tsohon na mai magana da yawun bakin kwamitin kamfen din Atiki Abubakar, Segun Sowunmi, ya caccaki tsohon ubangidansa kan yawan takarar da yake yi.

A labarin nan, za a ji cewa tsohon mataimakin gwamnan Jigawa, Alhaji Ahmed Mahmud Gumel ya zama jagoran ADC, kuma ya nemi matasa su shigo jam'iyyar.
Siyasar Najeriya
Samu kari