
Labaran NNPC







Aliko Dangote ya bayyana wadanda suke kokarin durkusa matatarsa bayan ya kai ziyara ga Bola Ahmed Tinubu. Dangote ya ce shugabannin NNPCL ba su cikinsu.

Mele Kyari, tsohon shugaban NNPCL ya bayyana cewa, ba a kama shi ba, kuma yana nan yana hutawa a gida. Ya bayyana cewa, ya kamata a daina yada jita-jita.

Tsohon shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kolo Kyari, ya bayyana cewa a shirye yake ya ba ds bayani kan yadda ya gudanar da shugabancinsa a kamfanin na mai.

Jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), sun tsare tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kolo Kyari, bayan fara bincike.

Rahotanni sun ce Hukumar EFCC na binciken tsofaffin shugabannin NNPC ciki har da Mele Kyari da wasu daraktocin matatun mai bisa zargin batar da N80bn.

Injiniya Bayo Ojulari ya sauke shugabannin matatun mai 3 a kasar nan, yana shirin farfaɗo da NNPCL bayan kashe kuɗi ba tare da ci gaba ba a zamanin Kyari.

Tsofaffin shugabanni a mulkin Muhammadu Buhari na fuskantar tuhumar rashawa; EFCC na binciken su bisa zargin wawure dukiyar kasa a mulkin Tinubu.

Kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL ya fara korar mutanen tsohon shugabansa, Malam Mele Kyari a wani sabon sauye sauye da Bayo Ojulari ya ɓullo da shi.

’Yan kasuwa, karkashin kungiyar IPMAN sun ce yanzu asara suke yi bayan NNPCL da Dangote sun sauke farashin fetur, yayin da talakawa ke amfana da ragin a kasuwa.
Labaran NNPC
Samu kari