
Majalisar dattawan Najeriya







Tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomhole ya ce Bola Tinubu zai yi nasara a zaben 2027. Ya ce ko yau aka yi zabe a Najeriya Bola Tinubu zai yi nasara.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai tilastawa 'yan adawa komawa APC.

Bayan kotu ta kama Farfesa Peter Oghan da laifin murde zabe, har yanzu yana yawo a gari ba tare da zaman kurkukun shekaru uku da aka yanke masa ba.

Majalisar dattawan Najeriya ta nuna damuwa kan karuwar hare-haren 'yan ta'addan Boko Haram. Ta bukaci a kara tura sojoji da kayan aiki jihohin Borno, Yobe.

An gabatar da kudirin karba-karba na shugaban kasa da mataimakinsa a yankuna shida na inda majalisar ta ƙi amincewa da kudurin dokar sauya kundin tsarin mulki.

Sanatocin Kebbi guda uku, Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya), Yahaya Abdullahi (Kebbi ta Arewa), da Garba Maidoki (Kebbi ta Kudu) sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Za ku ji a wannan rahoto cewa yan ta'addan Boko Haram na kwace makaman sojoji da aka sayawa da jami'an tsaro masu yawa, inji Dan majalisar Filato, Yusuf Gadgi.

Francess Ogbonnaya ta zargi Farfesa Sandra Duru da ba ta N300,000 domin ta ƙirƙiri sautin bogi da zai bata sunan Sanatar Kogis Natasha Akpoti-Uduaghan.

Tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya musanta zargin da aka jefe shi da shi na sanyawa a cafke wani dan mazabarsa bisa sukar ayyukansa.
Majalisar dattawan Najeriya
Samu kari