
Manyan Labarai A Yau







Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ikorodu a jihar Legas, Babajimi Benson, ya bayyana ba kananan hukumomi 'yancin cin gashin kai zai magance rashin tsaro.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da dakatar da hadiminsa saboda kalaman da ya yi dangane da batun sauya shekar Rabiu Musa Kwankwaso.

Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa an daure mahaifinsa saboda ya ki yarda a sanya shi makaranta lokacin da yake yaro.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kafa sababbin dokoki guda biyu a jihar. Daga cikin dokokin akwai ta haramta sare itacw ba bisa ka'ida ba.

Wani dan sanda ya saki wuta a wurin bincike ababen hawa a jihar Benuwai, harsashi ya yi ajalin wata daliba da ke ajin karshe a jami'a ranar Juma'a.

Hukumar tace fina finai ta jihar Kano ta sanar da haramta bikin ranar Kauyawa a fadin jihar. Ta bayyana cewa za ta dauki mataki kan duk wanda ya karya dokar.

Dakarun sojoji tare da hadin gwiwar mafarauta sun samu nasarar dakile harin 'yan ta'addan Boko Haram. Sojojin sun kashe 'yan ta'adda a yayin artabun.

Mutanen kauyen Isiagu Akpawfu da ke ƙaramar hukumar Nkanu ta Gabas a jihar Enugu sun fara shiga fargaba na naɗin sabon Igwe, lamarin ya kai kotun ɗaukaka kara.

Wata mata ta yanke al'aurar mijinta a Brazil ta hada miyar wake da ita da wasu sassan jikinsa. Matar ta ce ta aikata haka ne domin ta kama shi yana kallon batsa
Manyan Labarai A Yau
Samu kari