
Zaben jihohi







Sanata Buhari ya ce zai tsaya takarar gwamnan Oyo a 2027. Ya gaji da majalisa, ya ce ko an kawo tikitin sanata ba zai tsaya ba domin mutan ke son ya yi gwamna.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na neman a gyara tsarin zaɓe na ƙasa domin cire wa shugaban kasa ikon naɗa kwamishinonin zaɓe na jihohi (RECs).

Wanda ya yi takara a zaɓen fitar da gwani da gwamna a Anambra karkashin APC, Valentine Ozigbo ya maka jam’iyyar a kotu kan zaben, yana neman soke sakamakon.

Rahotanni sun fara bayyana cewa akwai yiwuwar bangaren CPC da ya shiga hadakar kafa jam'iyyar APC zai iya ficewa daga jam'iyya saboda salon mulkin Bola Tinubu.

Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Chikwuma Soludo, ya samu nasara zama halastaccen dan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APGA, ya yi godiya.

Yayin da APC ke shirye-shiryen zaben fidda gwani a jihar Anambara, akalla yan takara biyu sun sanar da janye daga zaben, ɗaya ya bar jam'iyyar gaba ɗaya.

Chief Chijioke Edeoga ya bayyana komawarsa PDP a matsayin dama ta haɗin kai a Enugu, ya ce lokaci ya yi da za a haɗa ƙarfi don nasarar jam’iyyar a zaben 2027.

Tsohon shugaban karamar hukumar Nassarawa, Auwalu Lawan Shuaibu Aronposu, ya bayyana yadda ya taimaka wa gwamnatin NNPP wajen dare wa mulkin Kano.

Majalisar wakilai ta amince da kudirin kirkirar sabbin kananan hukumomi, ciki har da Bende ta Arewa, Ughievwen, da Ideato ta Yamma, da wasu muhimman kudirori.
Zaben jihohi
Samu kari