
Hare-haren makiyaya a Najeriya







'Yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kai hari a Ijaha Ikobi, jihar Benue, inda suka kashe sojoji biyu da fararen hula biyu. An fitar da gawarwarkin daga yankin.

Dakarun rundunar sojin Najeriya ta kwato shanu sama da 1,000 da aka sace a jihar Filato. Sojoji sun yi artabu da 'yan bindigar da suka sace shanun tare da kashe biyu

Rikici tsakanin manoma da makiyaya a Nangere, Yobe ya yi sanadin mutuwar mutum daya da jikkatar wasu da dama, an kwato dabbobi 31 yayin da bincike ke ci gaba.

An samu barkewar rikicin manoma da makiyaya a wasu kauyukan jihar Taraba. Rikcin ya jawo an samu asarar rayukan mutane daga bangaren manoma da makiyaya.

'Yan bindiga sun kashe jigon APC da wasu mutum uku a Benue a wani harin kwantan bauna da suka kai garuruwa biyu. An ce wannan ne hari na biyu a cikin makonni biyu.

Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills ya gana da kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah domin jin matsalolin makiyaya a yankunan Najeriya da samar da mafita.

Kungiyar makiyaya ta sanar da cewa an kai hari kan shanu da wani makiyayi a karamar hukumar Riyom ta jihar Filato inda aka kashe shanu 37 da bindiga.

An tabbatar da cewa Kashim Shettima zai kai ziyara Filato Litinin, domin tattauna dabarun dawo da zaman lafiya bayan kashe sama da mutane 50 a jihar.

Ana fargabar cewa Fulani makiyaya sun kai hari a garin Gbagir, jihar Benue da safiyar Juma’a, sun kashe Kiristoci 10, sun jikkata 25, yayin da gwamnati ta yi martani
Hare-haren makiyaya a Najeriya
Samu kari