
Gwamnan Jihar Katsina







Gwamnatin jihar Ƙatsina ta fito ta yi bayani kan kudaden da ta kashe wajen samar da tsaro. Gwamnatin ta ce ta sayo kayan aiki tare da daukar ma'aikata.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa jama'a sun sami sauƙin matsalar tsaro a Katsina karƙashin Dikko Radda.

Ministan gidaje da ci gaban birane, Ahmed Dangiwa, ya bayyana cewa ya gamsu da kamun ludayin mulkin Gwamna Dikko Radda na Katsina. Ya ce ya cancanci komawa kujerar.

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya nuna kudirinsa na ganin ya kare martaba da mutuncin masarautun jihar. Ya ce suna da dadadden tarihi.

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya dawo gida Najeriya daga kasa mai tsarki. Gwamnan ya dawo ne bayan mahaifiyarsa ta riga mu gidan gaskiya.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jimamin rasuwar mahaifiyar gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda wacce ta rasu tana da shekara 93 a duniya.

'Yan bindiga sun farmaki kauyen Taka Lafiya a Katsina, sun kashe mutane biyu. Wannan na zuwa bayan da aka sace daliban jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma.

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana kudaden fansan da 'yan bindiga suka nema kan matashin mahaddacin Al-Kur'anin da suka sace a kwanakin baya a jihar.

'Yan fashi da makami sun kai hari makarantar sakandare ta Yashe a karamar hukumar Kusada a jihar Katsina. Sun kashe mai gadi a lokacin da ake suhur.
Gwamnan Jihar Katsina
Samu kari