
Dandalin Kannywood







Jarumin Kannywood, Malam Abdul Kano da aka fi sani da Baba Karkuzu rasuwa bayan rashin lafiya da ya yi fama da ita. Ali Nuhu ya sanar da rasuwarsa a Filato.

Shahararren jarumin fina-finan Kannywood, Abubakar Waziri ya ce da ba ya harkar fim, da ya zama malamin addini saboda yana da sha’awar gyaran al’umma.

Hukumar tace finafinai ta Kano ta dakatar da Samha M. Inuwa da Soja Boy bisa laifin tsiraici da batsa a bidiyo, tare da kwace lasisinsu. Mun yi bayani kan jaruman.

Jarumar masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Arewa watau Kannywood, Maryam Yahaya ta sayi sabuwar mota kirar Marsandi Benz, mutane sun taya ta murna.

Masu kallo sun roƙi a cire Firdausi Yahaya daga shirin Jamilun Jiddan, duk da haka ta zama fitacciya a fina-finai da ta samu kambun "Jaruma Mai Tasowa."

Usman Soja Boy ya ce Kannywood ba ta tsinana masa komai ba. Ya yi zargin shi ne ke taimakawa masana’antar, kuma dakatarwar ba za ta wani dame shi ba.

Allah ya karbi rayuwar mahaifiyar jarumi Yaya Ɗanƙwambo, an yi mata sutura a Samarun Zaria. Haka zalika, Mahaifin jarumi Baba Ari ya rasu, kuma an yi masa sutura.

Hadiza Gabon ta ce 'yan mata su daina damuwa da saurayinsu kawai, su auri mijin da ya dace, ko da mijin wata ne, a cewar wani sako daga Hassan Giggs.

Shekarar ta 2025 za ta zamo shekarar da za a ga sababbin finafinan Hausa da salon daukarsu ya sha bamban da na baya. Mun zakulo finafinai 6 da za a haska a 2025.
Dandalin Kannywood
Samu kari