An Kai Wike Bango, Ya Ce Zai Yi Murabus daga matsayin Ministan Abuja bisa Sharaɗi 1
- Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya fusata da kalaman tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi, wanda ya zarge shi da rashin gaskiya
- Wike ya roki shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya saki rahoton binciken NDDC, yana mai cewa idan har babu sunan Amaechi zai yi murabus
- Tsohon gwamnan ya ce matar Amaechi ta rika karɓar Naira biliyan 4 a kowane wata da sunan koyar da matan yankin Neja Delta sana'o'i
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya roƙi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya saki rahoton binciken hukumar Raya Neja Delta (NDDC).
Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya ce rahoton na kunshe da irin badakalar da ake zargin tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da hannu a ciki.

Asali: Facebook
Nyesom Wike ya yi wannan furucin ne a cikin shirin siyasa a yau na kafar Channels tv ranar Juma'a, 4 ga watan Yuli, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Nyesom Wike ya yi barazanar yin murabus
Ministan na Abuja ya sha alwashin cewa zai yi murabus daga mukaminsa idan har rahoton ya fito bai zargi Amaechi da hannu a karkatar da dukiyar ƙasa ba.
Wike ya yi wannan zargi ne a matsayin martani kan zargin cin hanci da rashawa da Amaechi, wanda shi ma tsohon gwamnan Ribas ne, ya tu masa.
Ya yi ikirarin cewa matar Amaechi na karɓar Naira biliyan 4 a kowane wata daga hukumar NDDC domin koyar da mata sana'o'i a yankin Niger Delta.
Mista Wike ya ƙara da cewa, ba kamar Amaechi ba, shi ya fito daga gida mai arziki ba gidan talakawa ba, shi ya sa yake da kudi gwargwadon hali da kuma jin daɗi.
Wike ya tona yadda matar Amaechi ta karɓi N4bn
“Da fari dai, matar Amaechi ba ‘yar kasuwa bace, ba ta taɓa zama haka ba. Shi ya sa nake roƙon Shugaban Ƙasa da ya saki rahoton binciken ƙwararru na NDDC.
"Kamfanin matar Amaechi na karɓar Naira biliyan 4 a kowane wata domin koyar da mata a yankin Niger Delta. Wannan yana nufin Naira biliyan 48 a shekara.
"Wannan rahoton yana nan, kun san wa ya danne rahoton tun farko? Malami, wanda a lokacin shi ne Antoni Janar. Yanzu yana cikin waɗanda suka koma gefe suna ɓaɓatu.”
- Nyesom Wike.

Asali: Facebook
Ministan Abuja ya roki Tinubu ya saki rahoto
Wike ya ce lokaci ya yi da Shugaba Tinubu zai taimaka wa ‘yan Najeriya ta hanyar bayyana gaskiyar lamarin.
"Tsohon Antoni Janar, Malami, shi ne ya kashe wannan magana domin kare wasu mutane. Ba wai surutu kawai nake ba, idan har abin da nake fada ba ya cikin rahoton, zan yi murabus daga matsayin ministan Abuja," inji shi.
Wike ya bayyana cewa matakin da matar Amaechi ta kai na zama ‘yar kasuwa ya samo asali ne daga karɓar biliyoyin Naira daga NDDC, ba ƙoƙarin ta ba ne, cewar Vanguard.
Wike ya caccaki haɗakar ƴan adawa a ADC
A wani labarin, kun ji cewa Nyesom Wike ya bayyana cewa haɗakar ƴan adawa a ADC ba ta ƙarfi ko tsarin da za ta iya kalubalantar shugaban ƙasa, Bola Tinubu a 2027.
Ministan Abuja ya ce kawancen ba shi da daidaito, kuma waɗanda suka kafa ta ba su da niyyar ceto Najeriya sai dai amfanin kansu.
Wike ya yi watsi da kawancen ADC, yana mai cewa PDP ce kaɗai ke da damar fuskantar APC idan ta daidaita kanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng