'Na Raina Albashin': Hadimin Sanata Ya Yi Murabus daga Muƙaminsa bayan Shekaru Tare
- Hadimin sanata a Ondo, Tunbosun Awe ya ajiye aikinsa a matsayin Mai taimakawa Jide Ipinsagba saboda albashin N20,000 da ake ba shi
- Awe ya ce tun 2007 Sanatan ke biyansa wannan kudin, duk da bukatarsa na karin albashi da yunkurin ganawa da 'dan majalisar ya ci tura
- Wani masoyin Sanatan ya kira Awe da "marar godiya", yana zargin shi da sauya bangare a siyasa saboda dalilan kansa na kashin kai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Akure, Ondo - Wani hadimin Sanata mai wakiltar Ondo ta Arewa, Tunbosun Awe, ya yi murabus daga mukaminsa.
Awe ya ajiye aikin ne saboda ana biyansa albashin N20,000 a wata kacal wanda ya ce ya yi kadan.

Asali: Original
Musabbabin murabus din hadimin Sanatan
Awe, wanda aka nada jami’in hulɗa da jama’a na Isowopo Ward II a Akoko ta Arewa maso Gabas, ya bayyana murabus dinsa a wata wasika a Akure, cewar Vanguard.
Ya ce wannan albashi bai yi daidai da yanayin tattalin arzikin yanzu ba balle sabuwar mafi ƙanƙantar albashi ta kasa wadda ya kai akalla N70,000.
Ya ce:
“Wannan ya biyo bayan albashin N20,000 da ka ke biya na, wanda bai dace da yanayin rayuwa da sabon mafi ƙarancin albashi.
“Bugu da ƙari, an nemi ganawa da kai a lokuta daban-daban domin a tattauna karin albashi, amma hakan bai samu ba.
“Musamman ma duba da cewa wannan albashi na N20,000 ne kake biyana tun lokacin da nake PA dinka tun 2007."

Asali: Facebook
Abin da Awe ya ce kan Sanatan Ondo
Awe ya bayyana dangantakarsa da Sanatan tun 2006 lokacin da ya kasance sakataren yakin neman zaben Sanata mai taken “Concept 2007”.
Ya koka cewa duk da kokarinsa na neman karin albashi, ba a saurare shi ba, kuma rayuwa ta kara tsanani fiye da da.
Awe ya ce ya taba yi wa Ipinsagba aiki a matsayin hadimi na musamman lokacin da yake rike da mukami a gwamnatin marigayi Gwamna Olusegun Agagu.
Ya nuna bacin ransa kan yadda ba a daga albashinsa ba shekaru da dama, duk da tashin farashin kayan masarufi da tsadar rayuwa.
Duk da haka, Awe ya gode wa Sanata bisa damar da ya ba shi na yin aiki tare da shi tun shekaru da suka gabata.
Mai magana da yawun Sanatan, Yinka Ajagunna, ba a iya samun sa domin jin ta bakinsa kan lamarin lokacin da aka tuntube shi ba.
Sai dai wani masoyin Sanatan, Bankole Akerele, ya ce Awe marar godiya ne, bai kamata ya kunyata Sanatan ba da irin wannan murabus.
Hadimin Gwamna Caleb ya yi murabus
Kun ji cewa wani jigo a gwamnatin Plateau ya yi murabus daga mukamin mai ba gwamnan jihar, Caleb Mutfwang shawara kan harkokin siyasa.
Letep Dabang ya ajiye mukaminsa a hukumance ranar 30 ga Yuni, 2025 inda ya tabbatar da komawa jam'iyyar APC.
Dabang ya bayyana godiyarsa ga damar da aka ba shi ya yi aiki da gwamnati, kuma ya ce yana fatan gwamnati za ta ci gaba da samun nasara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng