El Rufai Ya Yi Ikirarin yadda Jam’iyyar APC Ta Ke Sayen ’Yan Adawa Ana tsaka da Haɗaka
- Tsohon gwamann Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce APC ce ke kulla makirci domin hana hadin gwiwar jam’iyyun adawa kamar na ADC
- El-Rufai ya zargi gwamnati da amfani da kudi, mukami da hukumomi kamar EFCC domin yaudarar 'yan adawa ko a razana su
- Tsohon gwamnan ya ce gwamnatin yanzu na kashe dimokuradiyya, kuma kowa ya san matsalolin da APC ta jawo a PDP, LP da NNPP
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana kan hadakar jam'iyyun adawa bayan kaddamar da ADC a Abuja.
Nasir El-Rufai ya kuma tabo batun gwamnati mai ci da irin munafurcin da take kullawa jam'iyyun adawa a Najeriya.

Asali: Twitter
El-Rufai ya yi tone-tone kan gwamnatin APC
El-Rufai ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo yayin hira da jaridar RFI Hausa da ta wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Tsohon gwamnan ya ce babban matsalar jam'iyyun adawa ita ce APC saboda duk wata damuwa ita ta kulla.
Ya zargi jam'iyya mai ci da sayan wasu yan adawa wurin yi musu alkawura daban-daban domin yaudararsu zuwa cikinta.
El-Rufai ya ce:
"Wannan gwamnati tana amfani da abubuwa biyu domin take hakkin dimukradiyya a kasar nan'
"Na farko, suna neman mutane su sauya jam'iyya za su ba su shugabanci ko za su tabbatar zabe mai zuwa kana da tikiti ba hamayya.
"Ko kuma su ce kazo za a ba ka mukami ko ka kawo naka za a ba shi mukami ko zai samu kudi ko kuma su dauki kudin zunzurutu ma su baka.

Asali: Twitter
Zargin El-Rufai kan gwamnatin APC
El-Rufai ya kuma zargi cewa ana amfani da EFCC da ICPC da sauran hukumomi domin barazana ga yan adawa.
Ya kara da cewa:
"Idan haka bai yiwu ba sai a hada ka da EFCC a ce kana da matsala ko ICPC da sauransu, suna amfani da ma'aikatun gwamnati su zalunci al'umma.
"Kuma sun saka wasu alkalai a aljihu idan aka kai ka kara watakila a kai ka gaban wanda sun riga sun saka shi a aljihu."
El-Rufai ya ce duka wannan take-take ne na kashe dimukradiyya da kowace jam'iyya kuma kowane dan Najeriya ya san matsalar da ke cikin PDP.
Ya ce kowa a Najeriya ya san wanda ya shake wuyan PDP har ta kusan mutuwa haka kowa ya san waye ya kawo matsala a LP ta Peter Obi.
El-Rufai ya yi magana kan shirin hadaka
Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i ya bayyana dalilin da ya sa yan adawa suka rungumi ADC a madadin SDP.
Hakan ya biyo bayan manyan yan siyasa daga banagaren adawar kasar sun bayyana amfani da jam'iyyar ADC wajen cimma masufarsu a 2027.
Tsohon gwamnan ya ce an dauki ADC ne saboda saukin matsalolin cikin gida, amma duk da haka ana dakon INEC kan rajista sabuwar jam'iyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng