An Hana Su Atiku, Obi Ɗakin Taro a Abuja, Shirin Ƙaddamar da ADC Ya Gamu da Cikas
- Shirin kaddamar da ADC a matsayin jam'iyyar haɗakar 'yan adawa ya gamu da cikas a Abuja saboda otel din ya soke wurin taro
- An sanar da masu shirya taron cewa otel ɗin ba zai karɓi baƙuncin taron ba saboda "lamarin bin ka'idojin cikin gida," da ba a bayyana ba
- Dele Momodu ya zargi gwamnati da hannu a lamarin don tsoratar da 'yan adawa, amma ya ce hakan ba zai raunana ƙudirinsu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shirin kaddamar da ADC a matsayin jam'iyyar haɗaka ta 'yan adawar Najeriya ya gamu da cikas a ranar Laraba, sa'o'i kaɗan kafin a fara taron.
Otel din da aka shirya za a gudanar da zaman ya soke ba da aron dakin taronsa duk da cewa an riga da an biya kuɗin dakin taron gaba ɗaya.

Asali: Facebook
An hana su Atiku dakin taro a Abuja
Jaridar Punch ta rahoto cewa an shirya gudanar da taron ne a otel din Wells Carlton da ke Asokoro, Abuja, kafin aka zo aka samu wannan matsala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ana sa ran a wajen taron, za a gabatar da ADC a hukumance a matsayin jam'iyyar da za ta kalubalanci jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.
Sai dai, an sanar da masu shirya taron da safiyar Laraba cewa otel ɗin ba zai karɓi baƙuncin taron ba saboda wani "lamarin da ya shafi bin ka'idojin cikin gida" wanda ba a bayyana ba.
Sakon da otel din ya aika wa su Atiku
Wani sakon otel ɗin wanda sanannen ɗan jarida kuma ɗan siyasa Dele Momodu ya wallafa ranar Laraba a shafinsa na Instagram, ya bayyana cewa:
"Zuwa ga abokan huldarmu masu daraja, mun gode muku saboda zaɓar otel din Wells Carlton Hotel and Apartments matsayin abokin huldarku.
"Muna matuƙar nadamar sanar da ku cewa saboda wani lamarin da ya shafi bin ka'idojin cikin gida wanda yanzu muka samu labarinsa, ba za mu iya karɓar baƙuncin shirin ku da aka tsara ba.
"Mun san cewa nan da kasa da sa'o'i 24 ne shirin, don haka muna neman gafara sosai kan wannan sakon da zai zo maku bagatatan, muna ba da hakuri kan rashin jin daɗin da hakan zai iya haifar maku."
Martanin Dele Momodu kan hana dakin taron
Soke taron ba zato ba tsammani ya jawo martani mai tsanani daga manyan 'yan adawa, inda Dele Momodu ya yi zargin cewa akwai wata makarkashiyar siyasa a lamarin.
Momodu ya rubuta cewa:
"Gwamnati na ci gaba da amfani da duk wata damarta don tsoratar da 'yan adawa yayin da aka soke wurin taron kaddamar jam'iyyar ADC da hadakar 'yan adawa ta amince da ita.
Momodu ya kara da cewa:
"Amma wannan ba zai raunana jajircewar 'yan adawa ba waɗanda suka kuduri aniyar kalubalantar jam'iyyar mai mulki a 2027."

Asali: Facebook
"Ba ku da ikon saba yarjejeniya" - Lukman
A cikin wata sanarwa da aka haɗa a cikin wallafar Momodu, Salihu Lukman, a madadin kungiyar People and Passion Consult Ltd, ya zargi otel ɗin da keta yarjejeniyar da aka yi da shi.
"Wannan ba abin yarda ba ne. Ba da wani iko na saba yarjejeniya da aka amince da ita bisa doka kuma aka biya kuɗinta gaba ɗaya.
Wannan ba abin je ka-ka-dawo ba ne."
- Salihu Lukman.
2027: ADC ta zama jam'iyyar hadakarsu Atiku
Tun da fari, mun ruwaito cewa, kungiyar haɗakar jam’iyyun adawa ƙarƙashin jagorancin Atiku Abubakar ta amince da ADC a matsayin jam'iyyar kalubalantar APC a 2027.
An kuma naɗa tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark a matsayin shugaban riko, Rauf Aregbesola a matsayin sakatare, da Bolaji Abdullahi a matsayin kakaki.
Jagororin haɗakar, ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi da Nasir El-Rufai sun bayyana tabbacin cewa ADC za ta kayar da Bola Tinubu da APC a zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng