A ƙarshe, Atiku, El Rufai da Obi Sun Haɗe Kansu, Sun Zabi Jam'iyyar Doke Tinubu a 2027
- Ƙungiyar hadakar 'yan adawa da Atiku Abubakar ke jagoranta ta zaɓi ADC a matsayin jam'iyyar da za ta kalubalantar APC a 2027
- An naɗa David Mark a matsayin shugaba, Rauf Aregbesola matsayin sakatare da kuma Bolaji Abdullahi a matsayin kakakin ADC
- Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai sun nuna yakini cewa jam'iyyar ADC za ta doke Shugaba Bola Tinubu da APC a 2027
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Ƙungiyar hadakar 'yan adawa da Atiku Abubakar ke jagoranta ta zabi ADC a matsayin jam'iyyar da za ta yi amfani da ita wajen doke Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Wannan mataki ya biyo bayan ganawar da shugabannin ƙungiyar suka gudanar daga Talata zuwa Laraba, bayan jinkirin INEC na yi wa jam'iyyar da ƙungiyar ke so, watau ADA, rajista.

Asali: Twitter
Atiku, El-Rufai, Obi sun zabi jam'iyyar ADC
Tsohon sanatan Katsina ta Arewa, Ahmad Babba Kaita, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 1 ga Yuli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Sanarwar, wadda Dr. Uche Diala, daya daga cikin shugabannin ƙungiyar hadakar ta kasa (NCM) ya fitar, ta bayyana cewa:
“Muna sanar da ku cewa ƙungiyar hadakar 'yan adawa ta kasa (NCM) ta ɗauki ADC a matsayin jam'iyyarta domin tunkarar zaɓen 2027.”
“An cimma wannan matsaya ne a wani taron manyan shugabannin ƙungiyar da aka yi ranar 1 ga Yuli, 2025. Wannan shawarar ta samu amincewar dukkanin 'ya 'yanta."
David Mark ya zama shugaban hadakar ADC
Domin tabbatar da nasarar wannan matakin, shugabannin NCM sun amince da naɗa fitattun ‘yan siyasa a matsayin shugabannin rikon kwarya na jam'iyyar ADC:
Wadanda aka nada su ne:
- Tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa,
- Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam'iyyar na kasa,
- Tsohon ministan matasa da wasanni, Bolaji Abdullahi, a matsayin kakakin jam'iyyar
An ce nada wadannan ƙwararrun a matsayin shugabannin ADC zai tabbatar da cewa jam'iyyar 'yan adawar ta doke APC mai mulki a matakin kasa da ma jihohi.

Asali: Facebook
An aika sako ga 'yan takarar SDP da LP
A cewar sanarwar Dr. Uche Diala:
“Yana da muhimmanci mu sanar da magoya bayanmu da mambobin SDP cewa waɗanda suka riga suka shirya tsayawa takara a jam’iyyunsu kamar SDP da LP za su ci gaba da zama a can. Kuma ƙungiyar haɗin gwiwa za ta tallafa musu.
“Muna tabbatar maku da cewa wannan jam'iyyar ta haɗin gwiwa ta ginu ne a kan gaskiya, sadaukarwa da kishin ƙasa da shugabanninmu suka nuna.”
Rahoton jaridar Premium Times ya nuna cewa ƙungiyar za ta ci gaba da bin hanyoyin shari’a domin ganin an yi wa jam’iyyar ADA rijista.
Ƙungiyar adawar na kunshe da manyan jiga-jigan siyasa irin su Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai, Bukola Saraki, Rotimi Amaechi, Abubakar Malami da sauransu.
ADC: 'Za a tara miliyoyin kuri'u don doke Tinubu'
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar ADC ta bayyana shirin ta na tattara masu kada kuri’a miliyan 35 domin kalubalantar APC da Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ralphs Okey Nwosu, ne ya bayyana hakan yayin wani muhimmin taro da jam’iyyar ta gudanar a birnin tarayya Abuja.
ADC ta ce tana haɗa kai da ƙungiyoyin fararen hula da na matasa, tare da shirin kulla babban kawance da sauran jam’iyyu domin kifar da APC a gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng