Bayan Ganduje Ya Yi Murabus, Mutane 5,000 da Ke Goyon bayan PDP, LP Sun Koma APC

Bayan Ganduje Ya Yi Murabus, Mutane 5,000 da Ke Goyon bayan PDP, LP Sun Koma APC

  • Sama da mambobi 5,000 na LP, PDP, da APGA suka koma APC a Enugu, inda suka samu tarba daga ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji
  • Cif Nnaji ya nuna damuwa kan harajin da gwamnatin Enugu ta kakaba a jihar, wanda ya ce yana ƙara tsananta wahalar rayuwa
  • Ya yi alƙawarin samo ƙarin ayyukan yi da ababen more rayuwa daga tarayya ga jihar idan aka sake zaɓar Shugaba Bola Tinubu a 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Enugu - Gabanin zaben 2027, sama da mambobi 5,000 na jam’iyyun LP, PDP da APGA sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a jihar Enugu.

Ministan kimiyya da fasaha, Cif Uche Nnaji, tare da shugaban APC na Enugu, Cif Ugochukwu Agballah ne suka karɓi waɗanda suka sauya shekar a garin Aku, ƙaramar hukumar Igbo-Etiti a ranar Litinin.

Mambobin LP, PDP da APGA sun sauya sauya sheka zuwa APC a Enugu
Dubunnan magoya bayan jam'iyyun adawa a Enugu sun koma APC. Hoto: Labour Party, All Progressives Congress, People's Democratic Party
Asali: Facebook

Dubunnan mutane sun koma APC a Enugu

Sauran wadanda suka halarci taron sun haɗa da Hon. Sunday Umeha, wanda ke wakiltar mazabar Udi-Ezeagu a majalisar wakilai, da wasu jiga-jigan APC, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Yayin da yake jawabi a taron, Cif Uche Nnaji ya ce sauya shekar da ake yi zuwa APC alama ce da ke nuna cewa al'ummar Enugu sun fara fahimtar ayyukan da gwamnatin Bola Tinubu ke aiwatarwa.

Sai dai Nnaji ya nuna damuwarsa game da yadda ake yin abin da ya kira“ɓarnatar da dukiyar gwamnati da kuma kakaba haraji mai tsanani” a jihar Enugu.

Ya yi nuni da cewa wadannan matsaloli biyu su ne suka kara tsananta wahalar rayuwa a Enugu, karkashin gwamnatin Gwamna Peter Mbah.

"Yar talla na biyan harajin N100,000" - Minista

Ministan ya shaidawa mahalarta taron cewa:

“A yau a Enugu, muna fuskantar babban matsalar tattalin arziki. Mu ne na biyu a jihohi mafi tsadar rayuwa a Najeriya duk da cewa Enugu ta kasance garin ma’aikata.

“Yarinya da ke tallan ruwan leda na biyan harajin N300 zuwa N500 a kullum. Idan ka lissafa, tana biyan fiye da N100,000 a shekara.
“In dai za a yi amfani da wannan kuɗi yadda ya kamata, matasa da mata za su amfana da ilimi da lafiya kyauta, sannan za su samu kyawawan ababen more rayuwa.
“Amma abin takaici, a yau, babu waɗannan abubuwan saboda ba a amfani da harajin yadda ya kamata."
An roki al'ummar jihar Enugu da su zabi Shugaba Bola Tinubu da APC a zaben 2027
Jam'iyyar APC ta kara karfi Enugu yayin da minista ke rokon a zabi Shugaba Bola Tinubu a 2027. Hoto: @OfficialAPCNg, @officialABAT
Asali: Twitter

An roki Enugu ta zabi Tinubu, APC a 2027

Yayin da yake yabawa tsohon ɗan takarar majalisar dokoki a ƙarƙashin APGA, Celestine Attah, wanda ya jagoranci mambobin APGA, LP da PDP zuwa APC, Cif Nnaji ya yi alkawarin samar da karin ayyukan yi da kuma ababen more rayuwa daga gwamnatin tarayya.

Ministan ya ce APC a jihar ta shirya kanta domin karɓar ragamar mulkin jihar a 2027, inda ya roki jama’a su goyi bayan jam’iyyar da sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

“Da can APC tana aiki ne tamkar wata jam’iyyar kasuwanci a Enugu, inda ake amfani da ita wajen yin ciniki da PDP. Amma yanzu mun kori masu yi mata irin haka."

- Cif Uche Nnaji.

Ɗan majalisa, 'yan siyasa 10,000 sun koma APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar LP ta sake fuskantar babban koma baya a Enugu, yayin da wani ɗan majalisa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Hon. Sunday Umeha, wanda ke wakiltar mazaɓar Udi/Ezeagu, ya jagoranci wasu shugabannin LP ciki har da tsohon ɗan majalisa, zuwa APC.

Umeha ya bayyana cewa matakin nasa na sauya sheka ya biyo bayan niyyarsa ta mara wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya a gyaran Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »