Rikici, Matsaloli da Nasarorin da Ganduje Ya Samu a Shugabancin Jam'iyyar APC
A ranar Juma'a, 27 ga watan Yuni, 2027, shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga muƙaminsa, lamarin da ya girgiza siyasar Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Duk da ana ta surutu da ka-ce-na-ce kan dalilin da ya sa ya ɗauki wannan mataki, Ganduje ya ce ya ajiye muƙaminsa ne saboda dalilan da suka shafi kiwon lafiya.

Asali: Twitter
Jam'iyyar APC ta tabbatar da wannan lamari a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, ɗauke da sa hannun mai magana da yawun jam'iyyar, Felix Morka.
Wannan dai ya kawo ƙarshen tsawon watanni 22 da Ganduje ya yi yana shugabantar jam'iyyar APC tun bayan naɗinsa a watan Agusta, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
A cikin wasikar murabus ɗinsa, tsohon gwamnan na Kano ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa damar da ya ba shi ta jan ragamar APC a kujera lamba ɗaya.
Ganduje, mai shekaru 75, shi ne shugaban APC na shida tun bayan kafa ta a shekarar 2013 lokacin da jam'iyyun adawa suka yi hadaka, rahoton Gazette Nigeria.
Ya karɓi shugabanci ne daga Sanata Abdullahi Adamu, wanda ya jagoranci al’amuran jam’iyyar APC tun daga 2022 har zuwa zaɓen 2023 da aka yi.
A wannan rahoton, Legit Hausa ta zaƙulo muku abubuwan da suka faru ƙarƙashin jagorancin Ganduje, waɗanda suka kawo ci gaba ko akasin haka ga APC.
Ci gaba da nasarorin Abdullahi Ganduje a APC
Tun da aka kafa APC shekara 12 da ta wuce, babu lokacin da manyan ƴan siyasa suka sauya sheka zuwa jam’iyyar kamar lokacin da Abdullahi Umar Ganduje ke shugabanci.
A ƙarƙashin shugabancinsa, yawan mambobin APC ya ƙaru, kuma fitattun ’yan siyasa da dama sun koma jam’iyya mai mulki, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
1. Sauya shekar manyan jiga-jigan siyasa
A watanni biyu da suka gabata kacal, APC ta karɓi gobannonin jihohi biyu, Sheriff Oborevwori na jihar Delta da Umo Eno na Akwa Ibom, tare da mataimakansu.
Wani ƙarin babban jigo da APC ta samu shi ne Ifeanyi Okowa, tsohon gwamnan jihar Delta kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP a zaɓen 2023.
Jam'iyyar APC ta ƙara ƙarfi a Majalisar Tarayya, inda adadin sanatocinta ya ƙaru daga 59 da aka fara da su a watan Yunin 2023 zuwa 69 a ranar 25 ga Yuni, 2025.
A Majalisar Wakilai, APC na da kimanin kujeru 207 a yanzu, sabanin 175 da ta fara da su shekaru biyu da suka wuce, cewar rahoton Bussiness Day.
A gefe guda kuma, ana iya cewa ɗan siyasa mafi ƙima da APC ta rasa a cikin shekaru biyu da suka gabata shi ne Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna.
2. Nasarorin zaɓe da Ganduje ya samu
A ƙarƙashin jagorancin Ganduje, jam’iyyar APC ta samu nasarori a zaɓuka daban-daban da aka saba shiryawa daban da lokacin zaɓen gama gari.
Ɗaya daga cikin waɗannan nasarori shi ne wanda APC ta samu a Edo, inda Monday Okpebholo, tsohon Sanatan Edo ta Tsakiya, ya lashe zaɓen gwamna, ya karɓo jihar daga hannun PDP.
Tsohon shugaban jam’iyyar ya kuma jagoranci nasarar ci gaba da riƙe jihohin Kogi, Imo, da Ondo, inda aka gudanar da zaɓukan gwamna a lokuta daban-daban.
3. Sasanta rikice-rikicen jam'iyya
Ganduje ya warware rikice-rikicen siyasa da dama na cikin gida a jihohin da jam’iyyar APC ke mulki.
Ɗaya daga cikin irin waɗannan jihohi ita ce Ondo, inda rashin jituwa tsakanin marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu da mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, ya kusa tarwatsa jam’iyyar.
Kwamitin sasanci da ya kafa ne ya dakile rikicin kuma ya taimaka wajen samun nasarar APC a zaɓen gwamna na jihar.
4. Rajistar mambobin APC ta intanet
A ƙarƙashin Ganduje, APC ta kafa ofisoshi masu aiki a dukan mazabu 8,813 na ƙasar, tare da ƙaddamar da tsarin rajista ta intanet domin sauƙaƙa tattara bayanan mambobi a faɗin ƙasa.
Haka kuma, ya ƙaddamar da shirin kafa Cibiyar Nazarin Manufofin Ci gaba ta Ƙasa domin wayar da kan ƴan jam’iyya da jama’a game da shugabanci na dimokuraɗiyya.

Asali: Twitter
Duk da wasu abubuwan za a iya ɗaukarsu a matsayin nasarori, amma Ganduje ya gamu da masu jin haushinsa daga ciki da wajen APC tun da ya karɓi shugabanci.
Tsohon gwamnan ya ƙalubalanci waɗanda ke adawa da shi, kuma ya samu nasara a wasu daga cikin gwagwarmayar da ya yi.
Ruɗani da matsalolin da Ganduje ya fuskanta
An naɗa Ganduje a matsayin shugaban APC bayan tsohon Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Adamu, ya yi murabus.
An yi imanin cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya bada shawarar wannan naɗin, amma hakan bai yi wa bangaren Arewa ta Tsakiya na jam’iyyar daɗi ba, yankin da Adamu ya fito.
1. Ƙorafin yan Arewa ta Tsakiya a APC
Bayan murabus ɗin Adamu, yankin ya nemi a bar masa kujerar shugabancin bisa tsarin rabon madafun iko na jam’iyyar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Sai dai Ganduje ya yi ƙoƙarin shawo kan lamarin, wanda a watan Fabrairu, jam’iyyar daga yankin ƙarƙashin jagorancin Saleh Zazzaga ta nuna goyon baya da amincewa da jagorancinsa.
2. Zarge-zargen cin hanci da rashawa
Wata matsala da Ganduje ya fuskanta ita ce batun rashawa, duk da cewa batun bai da alaƙa kai tsaye da ofishin na sa na shugabancin jam’iyyar APC.
Ganduje ya fuskanci ƙararraki a kotu kan zarge-zargen cin hanci da rashawa, wanda ake tuhumarsa da sama da faɗi da dukiyar al'umma a lokacin yana gwamna.
Tun bayan barinsa ofis a 2023, gwamnatin Kano ta fara ƙoƙarin gurfanar da shi kan zarge-zargen cin hanci, ciki har da wasu da suka shafi iyalansa.
Ganduje ya samu nasara a wasu shari’o’in da gwamnatin Kano ta shigar da shi, wanda ya kai ga kotuna suka hana kama shi ko gurfanar da shi.
3. Dakatar da Ganduje a gundumarsa a Kano
Wani babban kalubale da Ganduje ya fuskanta lokacin da yake shugabancin APC shi ne dakatarwar da aka yi masa a gundumarsa da ke ƙaramae hukumar Dawakin Tofa a Kano.
Leadership ta kawo rahoton cewa shugabannin APC a gundumar Ganduje sun dakatar da shi ne bisa zargin cin hanci da ake yi masa.
Sai dai daga bisani wasu daga cikin shugabannin APC na gundumar sun ƙaryata lamarin, wanda ta kai ga shiga kotu kafin daga bisani aka warware matsalar.

Asali: Twitter
4. Zargin maida Najeriya jam'iyya ɗaya
Yawaitar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC ya jawo fargaba da korafe-korafe daga wasu mutane da jam’iyyu, suna nuna damuwa cewa Najeriya na dab da zama kasa mai jam’iyya ɗaya.
Amma Ganduje bai ga wani matsala da hakan ba. A cewarsa, babu laifi idan Najeriya ta koma jam’iyya ɗaya. Ya ce APC na da ikon ɗaukar duk masu sauya sheƙa zuwa cikinta.
“Ba muna cewa muna ƙaƙarin kawo tsarin jam’iyya ɗaya bane, amma idan wannan ne burin 'yan Najeriya, ba za mu yi musu gardama ba," in ji shi.
Wannan kalamai dai sun ƙara tayar da ƙura kan zargin yunƙurin APC na mayar da Najeriya ƙasar da jam'iyya ɗaya ke mulki, amma daga bisani komai ya lafa.
An dakatar da shugaban APC na Nasarawa
A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin APC na gundumar Gayam sun sanar da dakatar da shugaban jam'iyya na jihar Nasarawa, Hon. Aliyu Bello.
Wannan mataki na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan jagororin APC a matakin jihar Nasarawa sun kaɗa ƙur'ar amincewa da shugabancinsa.
Ana zargin shugaban APC na jihar Nasarawa da karya Sashe na 21 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng