'An Taso Kashim Shettima a Gaba': Ƴan Borno Sun Jefo Zargi bayan Murabus Ɗin Ganduje
- Wasu ‘yan jihar Borno sun koka matuka bayan murabus din Abdullahi Ganduje daga kujerar shugabancin APC
- Mafi yawan mazauna jihar sun ce haka wata dabara ce ta hana Kashim Shettima samun tikitin mataimakin shugaban kasa
- Sun bayyana cewa sauya shugabancin jam’iyyar APC daga Ganduje zuwa Borno zai iya kawo sauyi a tsarin yankin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - An fara samun zarge-zarge mabambanta kan ainihin dalilin murabus din Abdullahi Ganduje.
Wasu mazauna jihar Borno sun bayyana murabus din Abdullahi Ganduje daga shugaban jam’iyyar APC a matsayin wata maƙarƙashiya.

Asali: Twitter
Premium Times ta ruwaito wasu daga cikin yan jihar sun bayyana cewa hakan wata dabara ce ta hana Kashim Shettima tikiti a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Hasashen da ake yi kan murabus din Ganduje
Legit Hausa ta ruwaito cewa Ganduje ya yi murabus ba tare da tsammani ba, inda aka rantsar da Ali Dalori daga jihar Borno a matsayin shugaban riko.
Ko da yake Ganduje ya ce dalilin murabus dinsa shi ne rashin lafiya, jita-jita na cewa an tilasta masa ne saboda sauyin shugabanci kafin 2027.
Wasu kuma na zargin cewa ana neman ba jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso damar shiga jam'iyyar cikin sauki.
Ganduje: Mazauna jihar Borno sun yi hasashe
Yayin da wasu mazauna Borno suka taya Dalori murna, wasu sun ce sauyin shugabancin APC wata dabara ce don karbe kujerar mataimaki daga Arewa maso Gabas.
Wani dan siyasa daga Biu, Aliu Haidar, ya bayyana cewa akwai wata makarkashiya don tunbuke Shettima daga kujerar mataimakin shugaban kasa.
Ya ce:
“Idan aka ce za a bar Dalori a matsayin shugaban dindindin, hakan na iya nufin an shirya canza yankin da mataimaki zai fito."

Asali: Facebook
Ra'ayoyin mazauna Borno kan murabus din Ganduje
Abdulmajeed Monguno ya ce dokar jam’iyya na bukatar shugaban kasa, mataimakinsa da shugaban jam’iyya su fito daga sassa daban-daban na kasar.
Ya ce:
“Wannan na iya zama dabarar Tinubu-Kwankwaso don sauya mataimakin shugaban kasa zuwa yankin Arewa maso Yamma ko Arewa ta Tsakiya.”
Amma wasu mazauna Borno sun ce ba wai makarkashiya ake yi wa Shettima ba, sai dai an hukunta Ganduje ne saboda abin da ya aikata masa.
“Ganduje bai mara wa Shettima baya a taron shugabannin APC na Arewa maso Gabas ba, hakan ne ya jawo masa matsala."
- Cewar Muhammad Musa
Tattaunawar na nuna yadda ‘yan Najeriya ke kokarin fahimtar dalilin saukar wanda ke rike da babban mukami a jam’iyya mai mulki.
Peter Obi yabawa da murabus din Ganduje
Mun ba ku labarin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya yi magana bayan tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya yi murabus.
Peter Obi ya yaba wa Ganduje bisa murabus dinsa daga shugabancin jam'iyyar, yana mai cewa hakan abin koyi ne.
Tsohon gwamnan Anambra ya ce Ganduje ya dauki matakin da ya dace domin ya fifita lafiyarsa sama da duk wani mukami ko matsayi na siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng