APC Ta Tabbatar Murabus din Ganduje, Ta Fadi Dalilin Ajiye Kujerar da Ya Yi
- Jam’iyyar APC mai mulki ta tabbatar da murabus ɗin Dr Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam’iyyar na ƙasa
- Ta ce Ganduje ya miƙa takardar murabus ne domin ya mayar da hankali kan wasu muhimman al’amuransa na rayuwa
- Jam’iyyar ta yaba da ƙoƙarin Abdullahi Ganduje wajen haɓaka haɗin kan jam’iyya da tabbatar da nasarorin APC a ƙasa baki ɗaya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta tabbatar da murabus ɗin tsohon gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, daga matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
APC ta yaba da rawar da Abdullahi Ganduje ya taka wajen kawo hadin kai da wasu nasarori a lokacinsa.

Asali: Twitter
Leadership ta wallafa cewa sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Felix Morka, a daren Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Morka ya ce Ganduje ya ajiye mukamin ne da gaggawa domin kula da wasu muhimman al’amuransa na sirri.
Ganduje ya aika da takardar murabus ɗinsa ga Kwamitin Gudanarwar Jam’iyya ta ƙasa (NWC) ta hannun Sakataren jam’iyyar, Sanata Ajibola Basiru.
Ganduje ya godewa Tinubu yayin murabus
A cikin takardar murabus ɗin Ganduje ya nuna godiyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa goyon bayansa da ya samu tun daga lokacin da ya hau kujerar shugabancin jam’iyyar.
Ya bayyana cewa jagorancinsa na jam’iyya ya fara ne tun bayan murabus ɗin shugaban da ya gabace shi, Sanata Abdullahi Adamu a watan Agustan 2023.
Ganduje ya ce a lokacin da ya ke rike da wannan matsayi, ya himmatu wajen ƙarfafa haɗin kan jam’iyya da tabbatar da fahimtar juna tsakanin mambobi.
Jam’iyyar APC ta yaba da gudunmawar Ganduje
Jam’iyyar APC ta bayyana cewa Ganduje ya bar kujerar shugabanci da kwarin guiwa dangane da abubuwan da aka cimma a karkashin jagorancinsa.
APC ta ce ɗaya daga cikin nasarorin da aka samu a karkashin Ganduje shi ne samun sauya sheƙar jiga-jigan 'yan adawa da kuma tabbatar da sahihancin shugabancin APC a kotuna.

Asali: Twitter
Hanyar da APC za ta tafi a kai bayan Ganduje
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar ya tabbatar wa mambobi cewa jam’iyyar APC ba za ta ja da baya ba wajen aiwatar da kyakkyawan shugabanci da aka yi wa al’umma alkawari.
The Cable ta raohoto cewa jam’iyyar ta bayyana cewa za ta ci gaba da nuna jajircewarta a harkar mulki da tabbatar da ci gaban ƙasa da jin daɗin al’umma.
Jam’iyyar APC ta kuma yi addu’ar samun nasara da lafiya ga Ganduje a sauran fannoni na rayuwa da hidimar ƙasa baki ɗaya.
Dalori ya maye gurbin Ganduje a jam'iyyar APC
A wani rahoton, mun kawo muku cewa mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Alhaji Bukar Dalori ya maye gurbin Abdullahi Ganduje.
A yammacin Juma'a, 27 ga Yuni 2025 ne labarin murabus din Abdullahi Ganduje ya fito fili ba zato ba tsammani.
Ana hasashen cewa Alhaji Bukar Dalori wanda ya fito daga jihar Borno yana da alaka mai kyau da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng