An Naɗa Sabon Shugaban APC na Ƙasa Bayan Ganduje Ya Yi Murabus

An Naɗa Sabon Shugaban APC na Ƙasa Bayan Ganduje Ya Yi Murabus

  • APC ta naɗa Alhaji Bukar Dalori a matsayin muƙaddashin shugaban jam'iyya na ƙasa bayan Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus
  • Bukar Dalori, wanda shi ne mataimakin shugaban APC (Arewa) ya karɓi ragamar jam'iyyar ne bisa tanadin kundin tsarin mulki
  • A yau Juma'a, 27 ga watan Yuni, 2025, Ganduje ya ajiye shugabancin APC bisa wasu dalilai da ba a bayyana ba har zuwa yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa (Arewa), Alhaji Bukar Dalori, ya maye gurbin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi murabus ba zato ba tsammani.

Alhaji Bukar Dalori ya zama muƙaddashin shugaban APC na ƙasa sakamakon ajiye aikin Ganduje yau Juma'a kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanada.

Alhaji Bukar Dalori ya dare kujerar shugaban APC.
APC ta nada Alhaji Bukar Dalori a matsayin wanda zai maye gurbin Ganduje Hoto: Abdullahi Giggs
Asali: Facebook

Vangaurd ta tattaro cewa sashe na 14(2) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya yi bayanin ayyukan da suka rataya a wuyan mataimakin shugaban jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Daga cikin ayyuka har da taimaka shugaban jam'iyya na ƙasa wajen gudanar da ayyukansa bisa taarin doka.

Yadda Bukar Dalori ya maye gurbin Ganduje

A ƙarƙashin sashe na 14(2)(iii), kundin tsarin mulkin APC ya bayyana cewa:

“Mataimakin shugaban jam’iyya shi ke da alhakin riƙe kujerar shugaban jam'iyya na ƙasa idan ba ya nan."

Duk da har yanzu babu wata sanarwa a hukumance da ta yi bayanin dalilin murabus din Ganduje, wani babban jigo a APC ya shaida wa manema labarai cewa:

“Eh, gaskiya ne, ya yi murabus.”

Ganduje ya kwashe kayansa daga ofishin APC

Rahotanni sun nuna cewa hadiman Ganduje sun kwashe kayansa daga ofishin shugaban APC da ke hedkwatar jam’iyyar a Abuja kafin sanarwar.

Sai dai lamarin ya haifar da ruɗani da matukar mamaki tsakanin ma’aikata da baki a hedkwatar APC da ke Abuja saboda labarin ya zo masu kwatsam.

Majiyoyi sun bayyana cewa Ganduje ya yi murabus ne saboda dalilai na siyasa da ci gaban jam’iyya, musamman dangane da batun kujerar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Me yasa Abdullahi Ganduje ya yi murabus?

A rahoton The Cable, majiyar ta ce:

"Yanzu haka mutane da dama na ƙoƙarin su zama abokin takarar Shugaba Tinubu a 2027. Idan ka duba rahotannun da ke yawo, galibin sunayen da ake ambata sun fito ne daga Arewa maso Yamma.
"Idan aka ba wannan yanki mukamin mataimakin shugaban ƙasa, to dole ne shugaban jam’iyya na ƙasa ya fito daga wani yanki daban.
APC ta yi canjin shugabanci.
Jam'iyyar APC ta canza shugabanta na ƙasa yayin da ake tunkarar zaɓen 2027 Hoto: @OfficialAPC
Asali: Getty Images

Majiyar ta kuma tuna cewa dama asali an tsara kujerar shugaban APC daga Arewa ta Tsakiya, don haka akwai yuwuwar sabon shugaban jam’iyyar ya fito daga wannan yanki.

Da aka tambayi ko wanene zai maye gurbin Ganduje, wata majiya ta ce:

“Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umar Tanko Al-Makura, ne ke saman jerin sunayen da ake sa ran zai maye gurbin kujerar.”

Wani ɗan APC a Katsina, Umar Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan canjin shugabanci da aka samu ya nuna za a samu sauyi a tikitin 2027.

A cewarsa, alamu sun tabbatar da Shugaba Tinubu ba zai koma zango na biyu da mataimakin shugaban ƙasa, Ƙashim Shettima ba.

"Saukar da Ganduje ya yi tana da alaƙa da sauya Shettima, a tsarin APC ba za a ɗauki mataimaki a yankin da shugaban jam'iyya yake ba," in ji shi.

Makusancin Ganduje ya bar APC zuwa NNPP

A wani labarin, kun ji cewa Mustapha Bakwana, makusancin Abdullahi Ganduje, ya sauya sheƙa daga APC zuwa tafiyar Kwankwasiyya a Kano.

Bakwana ya ajiye muƙamkinsa na hadimin mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I..Jibrin, tare da komawa NNPP.

Mustapha Bakwana ya bayyana cewa ba su taɓa samun sabani da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »