Abin da Ƴan Najeriya Ke Cewa da Ganduje Ya Yi Murabus daga Shugabancin APC
- Ƴan Najeriya sun yi mamakin yadda kwatsam Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga kujerarsa ta shugaban APC na ƙasa
- Wasu na ganin dole akwai wata a ƙasa kuma da yiwuwar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya umarce shi da hakan
- Legit Hausa ta samu jin ta bakin wasu ƴan Najeriya kan wannan lamarin, inda da dama ke cewa akwai alamun shi zai zama abokin takarar Tinubu a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - A yau Juma'a, 27 ga watan Yuni, 2027, shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga kujerarsa.
Wannan al'amari dai ya girgiza siyasar Najeriya, domin babu wanda ya yi tsammanin Ganduje zai sauka daga shugabancin APC a daidai wannan lokaci.

Asali: Twitter
Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC
Rahoton The Cable ya nuna cewa wata majiya daga cikin jagororin APC ta tabbatar da lamarin, ta ce Ganduje ya ajiye aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad wanda shi ma ɗan asalin jihar Kano ne ya tabbatar da lamarim ya shafinsa na Facebook.
Bayan wannan labari ya karaɗe kafafen yaɗa labarai, yan Najeriya sun garzaya shafukan sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu kan murabus ɗin Ganduje.
Wasu na ganin cewa dole akwai wani dalili mai ƙarfi da ya sa ya ɗauki wannan matakin ko kuma umarnin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Wasu kuma kira suka yi ga shugaban ƙasa da ya ɗauki Ganduje a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2027 mai zuwa.
Martanin ƴan Najeriya kan matakin Ganduje
Legit Hausa ta tattaro muku wasu daga cikin martani ƴan Najeriya kan murabus din Ganduje, ga su kamar haka.
Iliyas Haruna ya ce:
"Ni a ganina ya kamata shugaban ƙasa ya ɗauki Ganduje a matsayin mataimakinsa a 2027."
Shu'aibu Sa'adu ya shaida wa wakilin Legit Hausa cewa:
"Ƙarshen siyasar Ganduje ta zo, dama shugabancin APC ne ƙarfinsa kuma yanzu ba kujerar, ni a hasashe na Kwankwaso ya kafa wannan sharaɗin kafin ya shigo APC."
Ahmad A. Muhammed ya danganta ci gaban da abin da ya faru a taron APC na shiryyar Arewa maso Gabas, inda ya ce:
"Masha Allah, mun ji daɗin haka, ai duk wanda ya taɓa Shettima to tashi ta ƙare a siyasa."

Asali: Facebook
Ajayi Samuel ya ce:
"Ya tabbata dai Tinubu ba zai tafi da Kashim Shettima ba a zaɓen 2027."
Wani matashi, Abdulkadir Musa ya shaida mana cewa alamu sun nun Ganduje ne zai zama abokin takarar Tinubu a 2027, wanda hakan ba zai wa ƴan Najeriya kyauba.
"Wannan alamu ne na shi za a ba takarar mataimakin shugaban ƙasa, idan haka ta faru to zamu shiga sabon babin wahalar rayuwa."
APC ta naɗa wanda zai maye gurbin Ganduje
A wani labarin kun ji cewa mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa (Arewa), Alhaji Bukar Dalori, ya maye gurbin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Alhaji Bukar Dalori ya zama muƙaddashin shugaban APC na ƙasa sakamakon ajiye aikin Ganduje yau Juma'a, 27 ga watan Yuni, 2025.
Ana ganin dai wannan mataki na canza shugabancin APC ba zai rasa nasaba da batun sauya mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng