Dalla Dalla: Abubuwan da Ake Buƙata wajen Kafa Sabuwar Jam'iyyar Siyasa a Najeriya

Dalla Dalla: Abubuwan da Ake Buƙata wajen Kafa Sabuwar Jam'iyyar Siyasa a Najeriya

Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa ta karbi wasikun buƙatu 110 daga ƙungiyoyin da ke neman rijistar zama jam'iyyun siyasa.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmud Yukubu ne ya bayyana hakan a taron da hukumar ta saba yi da shugabannin kafafen yaɗa labarai.

INEC ta karɓi bukatun kafa jam'iyyu.
Hukumar zabe INEC ta karɓi wasikun neman kafa sababbin jam'iyyu 110 daga kungiyoyi Hoto: @INECNigeria
Asali: Facebook

INEC ta tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter ranar Laraba, 25 ga watan Yuni, 2025.

Wannan na zuwa zuwa ne bayan haɗakar ƴan adawa ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ta nemi INEC ta yi jam'iyyar ADA rijista.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Jagororin adawar da suke shirin ƙirƙiro ADA sun haɗa ɗa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ɗan takarar LP a zaɓen shugaban kasar 2023, Peter Obi da sauransu.

Sai dai a jawabin da ya yi a Abuja, Farfesa Mahmud Yakubu ya ce dole kowace wasiƙar buƙatar kafa jam'iyya ta cika dokoki da ƙa'idojin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Yakubu ya ce:

“Ina sanar da ‘yan Najeriya, musamman masu sha’awar rajistar sababbin jam’iyyu, cewa littafin da ke ɗauke da ƙa’idoji da tsarin rajistar jam’iyyu na 2022 yana nan a shafin yanar gizon INEC.”

A wannan rahoton, Legit Hausa ta zaƙulo muku duka dokoki da ƙa'idojin kafa sabuwar jam'iyyar siyasa a Najeriya.

Sharuɗɗan rijistar sabuwar jam'iyya

Babu wata ƙungiya da INEC za ta yi wa rajista a matsayin jam’iyyar siyasa sai ta cika waɗannan sharudda tare da miƙa su zuwa ofishin shugaban hukumar zaɓe:

a) Sunaye, adireshin zamansu da jiharsu ta asali na mambobin kwamitocin gudanarwa na kasa da na Jihohi, tare da bayanan taron da aka gudanar inda aka zaɓi waɗannan shugabanni.

b) Bayanai na taron Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa da aka amince da suna, kundin tsarin mulki, manufofi, da tambari ko alamar jam’iyyar da ake ƙoƙarin kafawa.

c) Sunan ƙungiyar ko gajeriyar kalmarta wanda dole ne:

  • Kada ya zama iri ɗaya da sunan wata jam’iyya mai rijista ko wanda ya yi kama da wata jam’iyya da aka riga aka yi wa rajista, don gudun haifar da ruɗani a lokacin zaɓe.
  • Kada ya ƙunshi kowanne nau’in alamar ƙabila, addini, sana’a ko wani bangare da zai nuna wariya ko fifiko.

d) Dole ne jam’iyyar ta kasance tana da ofisoshi a akalla jihohi 24 daga cikin 36 da kuma babban ofishi a Birnin Tarayya Abuja.

e) Dole ne a samu akalla masu zaɓe 25 da aka yi rajistarsu a matsayin iyayen jam'iyya, waɗanda suka fito daga akalla kashi ɗaya bisa uku (⅓) na jihohin Najeriya da Abuja.

f) Tsarin Mulki: Dole ne jam’iyyar ta rubuta kundin tsarin mulki da ke bayyana tsarin jagoranci, manufofi, tsarin samun membobi, tsarin zaɓe da yadda ake hukunta mambobi.

g) Manufofin Jam’iyya: Wata takarda da ke bayyana manufofi da burin jam’iyyar.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu.
INEC ta jaddada cewa dole a bi ƙa'ida wajen yi wa jam'iyyu rijista Hoto: INEC Nigeria
Asali: Twitter

Tsari da ƙa'idojin rijistar sabuwar jam'iyya

1. Takardar niyya: A miƙa takardar nufin kafa jam’iyya zuwa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ke ɗauke da sunan jam’iyyar da ake so, tambari da taƙaitaccen suna.

2. Fom ɗin neman rijista: Cika da miƙa fom ɗin neman rajista (Form EC 15A) tare da waɗannan takardu:

  • Kundin tsarin mulki na jam’iyyar
  • Manufofi
  • Rajistar mambobi, wanda ya ƙunshi jerin sunaye, adireshi, lambobin waya, da imel na mambobin da za a kafa jam'iyyar da su.
  • Shaidar Hedikwata: Takardar mallaka ko haya ko wata shaidar zaman doka a wurin da aka ware a matsayin hedikwatar jam’iyyar.

3. Biya kuɗin rijista: Biyan kuɗin rajista da ba za a mayar ba na Naira miliyan ɗaya (₦1,000,000).

4. Miƙa takardu: Miƙa kwafi 50 na fom ɗin da aka cika, kundin tsarin mulki, da manufofi a cikin kwanaki 30 na aiki.

Tantancewar hukumar INEC

Bayan cika dukkan waɗannan sharuɗɗa da ƙa'idoji, tare da cike fom da miƙa takardar buƙata, hukumar INEC za ta bi ɗaya bayan ɗaya don tabbatar. da ba a karya doka ba.

INEC za ta bincike komai na sabuwar jam'iyyar da ake son kafawa, tun daga suna, tambari, kundin tsarin mulki d asuka abubuwan da aka ambata a sama don tabbatar da komai na kan doka.

Hukuncin hukumar zaɓe na ƙarshe

Bayan kammala bincike kan buƙatar kafa sabuwar jam'iyya da aka miƙa mata, INEC za ta ɗauki mataki na ƙarshe, wanda ya ƙunshi:

i) Idan INEC ta gamsu cewa ƙungiyar ta cika dukkan sharuddan da Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka gyara), dokar zaɓe ta 2022, da kuma waɗannan ka’idoji aka shimfiɗa, to za ta amince kungiyar ta zama jam'iyyar siyasa.

ii) Idan INEC ba ta gamsu cewa ƙungiyar siyasar ta cika dukkan sharuddan da ake buƙata ba, to ba za ta rajista ƙungiyar a matsayin jam’iyya ba.

Amma dole ne INEC za ta sanar da wannan ƙungiya cikin kwanaki bakwai daga cikin kwanaki 30 na aiki da aka tanada don rajistar ƙungiyoyin siyasa.

A takardar sanar da ƙungiyar, dole ne hukumar INEC ta bayyana a rubuce dalilan da suka sa ta ƙi rijistar sabuwar jam'iyyar siyasa.

A kundin ƙa'idojin da INEC ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta jaddada cewa duk wata ƙungiya da ke neman rijista da ta haɗa da ƙarya a bayananta, ba za a mata rijista ba.

Ta ce dole ƙungiyar siyasa ta cika dukkan sharuddan rajista da doka ta shimfiɗa cikin kwanaki 30 na aiki, daga ranar da ta karɓi fam daga hukumar zabe.

Da gaske ƙungiyoyi sun nemi yin rijista da INEC?

A wani labarin, kun ji cewa INEC ta bayyana cewa, har yanzu babu wata ƙungiya da ta gabatar da buƙatar rijistar sabuwar jam’iyyar siyasa a hukumance.

Mai magana da yawun INEC , Sam Olumekun, ya bayyana cewa, hukumar ta karɓi wasiƙun nuna sha’awa amma ba wai rijistar jam'iyya ba.

Olumekun ya ce duk wata ƙungiya da ke son ta zama jam’iyyar siyasa dole ne ta bi ƙa’idojin da doka da tsarin gudanarwar rajista suka shimfiɗa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »