PDP Ta Sake Yin Babban Rashi: Tsohon Shugabanta Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

PDP Ta Sake Yin Babban Rashi: Tsohon Shugabanta Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Tsohon shugaban PDP na Ebonyi, Dr Augustine Nwazunku, ya rasu wanda ya kasance malami a Jami’ar Nnamdi Azikiwe kafin rasuwarsa
  • Sanata Paulinus Igwenwagu ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce PDP ta dakatar da duk wasu taruka don girmama marigayin
  • PDP ta shirya ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayin a Aristocrat Hotel domin jajantawa yan uwa da kuma abokan arziki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abakaliki, Ebonyi - Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi babban rashi na tsohon shugabanta wanda aka tabbatar ta rasu a yau Alhamis.

Tsohon shugaban jam’iyyar a jihar Ebonyi, Dr Augustine Alugbala Nwazunku ya riga mu gidan gaskiya.

Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya mutu a Ebonyi
PDP ta yi rashin tsohon shugabanta a Ebonyi. Hoto: People's Democratic Party, Ebonyi State.
Asali: Facebook

Mukaman da marigayin ya rike kafin rasuwarsa

Rahoton Tribune ta ce kafin rasuwarsa, Dr. Nwazunku, ya tsaya takarar gwamna a karkashin PDP a zaben 2023 da aka gudanar wanda APC ta yi nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Har ila yau, ya koyar a matsayin malami a Jami’ar Nnamdi Azikiwe a Awka da ke jihar Anambra wacce ke yanki ɗaya da Ebonyi a Kudu maso Gabas a Najeriya.

Sanata Paulinus Igwenwagu, wanda ya kasance ɗan takarar mataimakin gwamna a PDP a 2023, shi ya tabbatar da labarin mutuwar.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ta dakatar da duk wani aiki da aka tsara don girmama marigayin duba da irin gudummawar da ya ba jam'iyyar wanda ba zai misaltu ba.

Ya ce:

“Ina kwananku, da fatan an tashi lafiya, mutanen PDP, musamman reshen jihar Ebonyi.
"A madadin jagoranmu, Dr. Ifeanyi Chukwuma Odii, da dukkan PDP na Ebonyi, muna sanar da ku cewa mun sake rasa ɗaya daga cikinmu.
"Marigayin ya kasance jagora, mamba mai aminci kuma tsohon shugaban rikon kwarya na jam’iyyarmu a Jihar Ebonyi, Farfesa Augustine Nwazunku.”
PDP ta rasa shugabanta a jihar Ebonyi
Tsohon shugaban PDP a Ebonyi ya koma ga Allah. Hoto: Legit.
Asali: Original

Jam'iyyar PDP ta dakatar da wasu tarukanta

Dalilin haka, jam’iyyar PDP ta ce duk wasu taruka da aka shirya ranar Asabar, 28 ga Yuni, 2025, an dakatar da su saboda mutunta iyalan marigayin a jihar.

An gayyaci mambobi zuwa 'Aristocrat Hotel' a kan titin Ezza domin tafiya zuwa ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayin wanda ya rasu a yau Alhamis 26 ga watan Yunin 2025.

Har yanzu ba a bayyana musabbabin mutuwarsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton a yammacin yau Alhamis 26 ga watan Yunin 2025.

Dr. Nwazunku ya shahara wajen hidima ga jam’iyya, ilimi da lafiyar jama’a an ce rashinsa babban gibi ne ga PDP a Ebonyi.

Tsohon shugaban PDP ya koma APC a Ebonyi

A baya, mun ba ku labarin cewa jam'iyyar APC reshen jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabas ta karɓi tsohon shugaban PDP da magoya bayansa da suka koma cikinta.

Barista Ufeanyi Nworie tare da wasu kusoshin PDP da ɗumbin magoya baya sun sauya sheka zuwa APC don ba da gudummuwa wajen kawo ci gaba.

A taron da aka shirya domin tarbarsu, shugaban APC ya buƙaci su ba Gwamna Francis Nwifuru haɗin kai a ƙoƙarinsa na ɗaga darajar jihar Ebonyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »