Gwamna Radda Ya Yi Magana kan Zama Abokin Takarar Tinubu a 2027

Gwamna Radda Ya Yi Magana kan Zama Abokin Takarar Tinubu a 2027

  • Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa yana da burin zama mataimakin Shugaba Bola Tinubu
  • Dikko Umaru Radda ya nesanta kansa daga jita-jitar da ke danganta shi da neman maye gurbin Kashim Shettima
  • Gwamnan ya bayyana cewa a yanzu hankalinsa yana kan sauke nauyin da mutanen jihar Katsina suka ba shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya nesanta kansa daga rahotannin da ke danganta shi da burin zama mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Gwamna Dikko Radda ya bayyana hakan ne tare da jaddada cewa hankalinsa gaba ɗaya yana kan yi wa al’ummar jihar Katsina aiki ne kawai.

Gwamna Radda bai son zama mataimakin Tinubu
Gwamna Radda ya ce bai da burin zama mataimakin Tinubu a 2027 Hoto: @DOlusegun, @dikko_radda
Asali: Twitter

Bayanin ƙaryata jita-jitar ya fito ne daga bakin babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Sanarwar ta ce Gwamna Radda ya yi jawabin ne a garin Dutsin-Ma yayin wani taron da ƙungiyar Dutsin-Ma Development Forum ta shirya a ranar Talata.

Me Radda ya ce kan zama mataimakin Tinubu?

Yayin da yake magana kan jita-jitar, gwamnan ya ce ya lura da wasu hotunan talla da ke nuna cewa yana neman wani muƙamin.

“Na ga hotuna da saƙonni da ke nuna wai ina neman wani muƙami daban."
“Ina so na fayyace muku cewa, na nemi izinin ku ne domin na yi wa jihar Katsina hidima a matsayin Gwamna, kuma wannan shi ne abin da na sa a gaba."
“Ba ni da hannu a kowane irin kamfen ko yunƙuri na neman wani muƙami a wani wuri. Aiki na shi ne na sauke amanar da kuka danƙa mani."

- Dikko Umaru Radda

A baya-bayan nan ne dai majalisar dokokin jihar Katsina ta bayyana goyon bayanta ga Gwamna Radda domin ya zarce kan wa’adin mulki na biyu.

Hakazalika, Sanatoci da ƴan majalisar wakilai daga jihar Katsina suma sun mara masa baya.

Gwamna na son samar da zaman lafiya a Katsina
Gwamna Radda ya ce yana son sauke nauyin da mutanen Katsina suka ba shi Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Gwamna Radda ya maida hankali kan tsaro

Gwamna Radda ya kuma jaddada ƙudirinsa na tabbatar da zaman lafiya a jihar Katsina.

“Batun tsaro shi ne babban abin da muka fi ba fifiko mulkinmu. Muna aiki tuƙuru ba dare ba rana domin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a Katsina."
"Ba za mu rika yin alkawarin da ba za mu iya cikawa ba, kuma dukkannin shawarwarinmu za su ci gaba da kasancewa bisa gaskiya da tsoron Allah."

- Gwamna Dikko Umaru Radda

Jingir ya kafa sharaɗin zaɓen Tinubu a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen malamin addinin musulunci, Sheikh Sani Yahaya, ya kafa sharaɗin goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Sheikh Jingir ya bayyana cewa ba zai marawa Tinubu baya ba, muddin ya ajiye Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa.

Kalaman Sheikh Jingir dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da jita-jitar cewa akwai yiwuwar Shugaba Tinubu ya maye gurbin Shettima gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta [email protected]

OSZAR »