Ana Shirin Tarar wa Tinubu, INEC Ta Faɗi Sababbin Jam'iyyun da Aka Nemi Rijista kafin 2027

Ana Shirin Tarar wa Tinubu, INEC Ta Faɗi Sababbin Jam'iyyun da Aka Nemi Rijista kafin 2027

  • Hukumar zaɓen Najeriya watau INEC ta ce kungiyoyi 110 sun rubuta wasiƙar buƙatar yi masu rijistar zama jam'iyyun siyasa
  • Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmud Yakubu ya ce za su fitar da jerin sunaye, tambari da shugabanni riko na waɗannan jam'iyyu
  • Ya yi gargaɗin cewa dole ne kowace kungiya da ke son zama jam'iyyar siyasa ta cika duka sharuɗɗa da dokokin da aka shimfiɗa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta karɓi wasiƙun buƙata daga kungiyoyi 110 da ke son rajista a matsayin jam’iyyun siyasa.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin taron hukumar da shugabannin kafafen yaɗa labarai a Abuja.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu.
An nemi yi wa sababbin jam'iyyu 110 rijista da INEC kafin 2027 Hoto: INEC Nigeria
Asali: Getty Images

Farfesa Yakubu ya ce hukumar INEC na ci gaba da nazarin buƙatun bisa tanadin doka da kuma dokokin tsarin gudanarwa, kamar yadda Leadership ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

INEC ta karɓi buƙatun rijistar jam'iyyu 110

Ya ƙara da cewa hukumar INEC ta tabbatar da karɓar duka buƙatun da aka tura zuwa yanzu, ban da guda shida da aka turo mata kwanan nan, waɗanda za a tabbatar kafin ƙarshen mako.

“Zuwa ranar Litinin, 23 ga Yuni, 2025, INEC ta karɓi wasiƙun buƙata daga kungiyoyi 110 da ke son yin rajista a matsayin jam’iyyun siyasa.
"Muna gudanar da bincike da nazarin waɗannan buƙatu da kyau bisa ga tanadin dokokinmu da ƙa’idojin gudanarwa.
"Mun tabbatar da karɓar duka buƙatun da aka tura zuwa yanzu ban da guda shida da aka kawo mana kwanan nan, waɗanda za a tabbatar ingancinsu kafin ƙarshen mako.”

- Farfesa Mahmud Yakubu.

Shugaban INEC ya faɗi dokokin kafa jam'iyya

Shugaban INEC ya kuma jaddada cewa duk wani mai sha’awar kafa sabuwar jam’iyyar siyasa zai iya samun littafin ƙa’idoji da tsarin rajistar jam’iyyun siyasa (2022) a shafin yanar gizon hukumar.

“Ina sanar da ‘yan Najeriya, musamman masu sha’awar rajistar sababbin jam’iyyu, cewa littafin da ke ɗauke da ƙa’idoji da tsarin rajistar jam’iyyu na 2022 yana nan a shafin yanar gizon INEC.”

INEC za ta fitar da sunayen sababbin jam'iyyu

Ya ƙara da cewa hukumar za ta saki cikakken jerin sunayen kungiyoyi 110 da ke neman rajista a matsayin jam’iyyun siyasa, rahoton The Cable.

A cewarsa, jerin zai ƙunshi sunayen da suka raɗawa jam'iyyun, gajerun sunaye, adireshinsu, tambura da kuma sunayen shugabanni da sakatarori na riko.

Shugaban INEC ya gana da ƴan jarida.
INEC za ta saki sunayen sababbin jam'iyyun da ake nemi rijista Hoto: @INECNigeria
Asali: Twitter
“Domin tabbatar da gaskiya da bai wa jama’a bayani, za mu dora jerin sunayen kungiyoyin da ke neman rajista a shafinmu na yanar gizo da kuma kafafen sada zumunta ba da jimawa ba.
"Haka kuma, mun haɗa kwafin takardun a cikin fayil ɗin ku na wannan taro,” in ji Farfesa Yakubu.

Ƴan adawa na da shakku kan hukumar INEC

A wani rahoton, kun ji cewa Nasir El-Rufai ya bayyana cewa haɗakar ƴan adawa na da shakku game da yiwuwar samun rajistar sabuwar jam’iyya a INEC ta yanzu.

Tsohon gwamnan na Kaduna ya ce INEC karkashin Farfesa Mahmud Yakubu ba ɗaya take da hukumar da suka sani a baya ƙarƙashin Farfesa Attahiru Jega ba.

Haɗakar manyan jagororin adawar Najeriya ciki har da El-Rufai sun miƙa buƙatar yi wa sabuwar jam'iyya mai suna ADA rajista ga hukumar zaɓe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »