Abin Boye Ya Fito Fili: Shugaban SDP Ya Fallasa Masu Kitsa Rikici a Jam'iyyar
- Shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa ya sanya ƙafa ya yi fatali da batun sakatarwar da aka yi masa daga muƙaminsa
- Alhaji Shehu Gabam ya bayyana cewa har yanzu yana nan darama a kan muƙaminsa na shugaban jam'iyya
- Gabam ya nuna yatsa ga haɗakar ƴan adawa kan kunna wutar rikici a jam'iyyar bayan sun kasa ƙwace ta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Rikicin da ya girgiza jam’iyyar adawa ta SDP ya ɗauki sabon salo, bayan da aka dakatar da shugaban jam'iyyar na ƙasa, Alhaji Shehu Gabam.
Alhaji Shehu Gabam ya ƙaryata dakatarwar da aka ce an yi masa daga muƙaminsa, yana mai bayyana hakan a matsayin labarin ƙarya da ya kamata a yi watsi da shi.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a ranar Talata a hedkwatar jam’iyyar ta ƙasa dangane da dakatarwar da ake zargin an masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
"Har yanzu ni ne shugaban SDP na ƙasa kamar yadda kuke gani."
- Alhaji Shehu Gabam
Gabam ya nuna yatsa ga ƴan haɗaka
Gabam ya zargi haɗakar ƴan adawa da wasu daga cikin jami’an jam’iyyar na ƙasa da hannu a rikicin da ke afkuwa a jam’iyyar SDP.
Ya bayyana cewa babu wani taron hukuma na kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) da aka gudanar inda aka yanke irin wannan hukunci, yana mai tambayar daga ina wannan sanarwar ta samo asali.
A cewarsa, wani kamfanin lauyoyi mai zaman kansa ne ya tuntuɓi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) domin neman izinin gudanar da taron kwamitin NWC.
Ya ce sakataren jam’iyyar na ƙasa, Dr. Olu Agunloye ya rattaɓa kan takardar, amma hukumar ta ce ba za ta amince da hakan ba saboda babu sa hannun shugaban jam’iyyar a ciki.
Gabam ya ce INEC ta bayyana wannan buƙata daga sakataren jam’iyyar a matsayin wacce ba bisa doka ba, domin babu sa hannunsa a ciki.
Yayin da yake bayyana damuwarsa kan rikicin, Gabam ya zargi ƴan haɗaka da ke so su mamaye jam’iyyar da ƙulla makirci don lalata SDP tun da sun kasa mallaketa.
“Ina ganin mun taɓa fuskantar irin wannan rikici a baya. Yanzu yana sake bayyana. Wasu daga cikinmu mun san inda wannan rikicin ke fitowa daga ciki, saboda wannan haɗakar da wasu mutane a cikinta sun ƙudiri aniyar cewa ko dai su ƙwace SDP ko kuma su jefa ta cikin rikici."
"Akwai gagarumar matsin lamba daga fannoni daban-daban da ke ganin SDP a matsayin babbar barazana da ba za su iya sarrafawa ba."
- Alhaji Shehu Gabam

Asali: Twitter
Shugaban SDP ya roƙi Bola Tinubu
Sai dai ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya umarci hukumomin tsaro na ƙasa da su guji bari ƴan siyasa su riƙa amfani da su wajen ruguza dimokuraɗiyya, rahoton The Punch ya tabbatar.
"Wannan lamari yana da matuƙar haɗari ga dimokuraɗiyyarmu. Duk lokacin da muka samu shugabanni da ba sa iya jurewa masu sukar gwamnati, to al’umma ta lalace. Dimokuraɗiyya za ta ɓace."
Ƴan daba sun farmaki hedkwatar SDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan daba sun farmaki hedkwatar jam'iyyar SDP ta ƙasa da ke Abuja.
Ƴan daban sun kai farmakin biyo bayan dakatar da shugaban jam'iyyar na ƙasa, Alhaji Shehu Gabam daga muƙaminsa.
Ƴan jaridan da ke kawo rahoto daga hedkwatar sun ji a jikinsu bayan harin da ƴan daban suka kai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng