An yi wa Tinubu Alkawarin Kuri'a Miliyan 2.5 yayin da 'Yan Adawa ke Kara Hada Kai

An yi wa Tinubu Alkawarin Kuri'a Miliyan 2.5 yayin da 'Yan Adawa ke Kara Hada Kai

  • Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya ce zai sama wa Shugaba Bola Tinubu kuri’a miliyan 2.5 a zaben 2027
  • Monday Okpebholo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi sababbin ‘yan jam’iyyar APC daga PDP a Esan ta Tsakiya
  • Sanata Okpebholo ya ce wannan mataki na nuna godiya ne bisa ayyukan cigaba da Tinubu ke aiwatarwa a jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya sha alwashin bai wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kuri’a miliyan 2.5 a babban zaɓen 2027.

Monday Okpebholo ya ce zai yi haka ne a matsayin wata hanya ta nuna godiya bisa yadda shugaban ya nuna ƙauna da kulawa ga jihar.

Gwamnan Edo ya ce za su sakawa Tinubu da kuri'u a 2027
Gwamnan Edo ya ce za su sakawa Tinubu da kuri'u a 2027. Hoto: Bayo Onanuga|Edo State Government
Asali: Facebook

Rahoton Tribune ya nuna cewa Okpebholo ya bayyana hakan ne a wajen taron maraba da sababbin ‘yan jam’iyyar APC daga jam’iyyar adawa ta PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

APC ta karɓi sababbin ‘yan PDP a Edo

A yayin bikin karɓar sababbin ‘yan jam’iyyar PDP, Okpebholo ya jinjina wa matakin da suka ɗauka na sauya sheƙa zuwa APC.

Gwamnan ya jinjina musu yana mai cewa hakan hujja ce ta wanzuwar sauyi a siyasar Esan ta Tsakiya da jihar Edo gaba ɗaya.

Punch ta wallafa cewa ya ce:

“Ina taya sababbin ‘yan jam’iyyar APC murna, waɗanda suka yanke shawarar komawa cikin wannan babbar jam’iyya ta mu.
"Wannan sauya sheƙa alama ce ta rashin ƙarfin jam’iyyar PDP a Esan ta Tsakiya, wanda shi ne ma yankina.”

Ya ƙara da cewa:

“Yau siyasar PDP ta kare a wannan karamar hukuma. Matakin da suka ɗauka na shiga APC ya nuna amincewarsu da shugabancin mu da ci gaban da muke kawowa.”

Za a samawa Tinubu kuri'a miliyan 2.5 a Edo

Gwamna Okpebholo ya bayyana cewa goyon bayan al’umma ga gwamnatin APC da shugabancin Tinubu zai bayyana a fili a babban zaɓen 2027.

Sanata Okpebholo ya ce za su tabbatar da bai wa shugaban ƙasa kuri’a miliyan 2.5:

“A shekarar 2027, za mu saka wa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa ƙaunar da yake yi wa jihar Edo ta hanyar ba shi kuri’u miliyan 2.5.
"Mutane sun riga sun bayyana matsayinsu ta nuna mana goyon baya. Edo ta APC ce, APC kuma ita ce hanyar ci gaban mu."

Ya ƙara da cewa:

“Ba zan ci amanar ku ba. Zan ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da cigaban da jihar mu ke samu ya dore.”
Gwamnan Edo ya ce PDP ta musu a jiharsa
Gwamnan Edo ya ce PDP ta musu a jiharsa. Hoto: Edo State Government
Asali: Twitter

Nkem Blessing ta tattauna da Legit

Wata matashiya daga jihar Edo, Nkem Blessing ta zantawa Legit Hausa cewa mutanen jihar ne za su yanke hukuncin zabe ba gwamna ba.

"Bana tunanin za a samu mutane miliyan 2.5 da za su fito zabe balle a ce an samawa shugaban kasa kuri'un.
"Amma dai hukunci yana hannun masu zabe."

Tsofaffin magoya bayan Tinubu sun ziyarci Atiku

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya gana da wasu 'yan siyasa domin tattauna maganar kayar da Bola Tinubu.

Atiku Abubakar ya gana da wasu 'yan siyasa daga Arewa ta Yamma da suka ce sun yi nadamar goyon bayan Tinubu a zaben da ya wuce.

Ya bukaci 'yan siyasar su cigaba da jajircewa wajen ganin an hada kai domin magance matsalolin Najeriya, musamman sauya gwamnati a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »