'Tinubu ba zai Kai Labari ba,' El Rufa'i ya Fadi Abubuwan da za Su Hana APC Nasara a 2027
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce Bola Tinubu ba zai ci zaben 2027 ba, kuma da wuya ma ya zo na uku a zaben da za a fafata
- El-Rufa'i ya ce haka ne bayan ya daina goyon bayan gwamnatin ta APC saboda matsalolin tattalin arziki da tsaro da ke addabar mulkinta
- Ya ce gwamnatin Tinubu ta fi ta Muhammadu Buhari tabarbarewa, ya ce adadin wadanda aka sace da kashe wa a 2024 ya fi na shekarun Buhari
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da wata dama ta samun nasara a zaben shugaban kasa na 2027.
El-Rufai ya bayyana haka ne a ranar Litinin, inda ya ce raunin tattalin arziki da tabarbarewar tsaro na daga cikin manyan dalilan da za su hana Tinubu zarcewa.

Asali: Facebook
A hira da ya yi da Arise News, El-Rufa'i ya ƙara da cewa rashin ci gaba a fannin gine-gine da ayyukan raya kasa ya sa ‘yan Najeriya da dama suka karaya da gwamnatin APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
El-Rufa’i: ‘Ba za a zabi Bola Tinubu ba'
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa El-Rufai, wanda ya goyi bayan Tinubu a zaben 2023, ya ce sababbin bincike sun nuna cewa mutane da dama sun gaji da gwamnatin tarayya.
Ya ce:
“Na taɓa cewa a wasu sassan ƙasar nan, musamman Kudu maso Gabas da Arewa, Tinubu na da kaso 91% na rashin amincewar jama’a. Ko a Lagos, yana da 78% na rashin karbuwa.”

Asali: Facebook
Ya ƙara da cewa:
“Eh, a wasu jihohin Kudu maso Yamma kamar Ondo da Ekiti yana da ɗan sauƙi, amma ko a can babu inda ya samu 50% na amincewa. Ta kare wa Tinubu.”
Gwamnatin Tinubu ta gaza — El-Rufai
Nasir El-Rufa'i ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu ta fi ta Buhari lalacewa, duk da cewa da farko ya yi tsammanin zai yi abin azo a gani.
A cewarsa:
“Da ka tambaye ni a shekarar 2022 ko 2023 lokacin da muke kamfe, cewa abubuwa za su tabarbare haka, da na ce kana da matsala a kwakwalwa.”
“Fiye da mutane miliyan 2.2 aka sace, kuma sama da 615,000 sun mutu. Nigeria tana yaki ne? Wannan ya fi abin da ya faru a cikin shekaru takwas na Buhari cikin shekara guda.”
Duk da shaidar rashin jin daɗinsa da gwamnatin yanzu, El-Rufai bai tabbatar da ko zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027 ba.
Sai dai ya ce abin da ya fi mai da hankali a kai yanzu shi ne tabbatar da samun kyakkyawan shugabanci a Najeriya.
El-Rufa'i ya caccaki gwamnatin APC
A baya, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake bayyana matsayinsa kan dangantakarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa gwamnonin Arewa na jam’iyyar APC ne suka yanke shawarar mika mulki zuwa Kudu bayan shekaru takwas na mulkin Muhammadu Buhari.
Ya kara da cewa ya yi nadamar nuna goyon baya har gwamnatin APC, karkashin Bola Tinubu ta samu nasara, ganin tarin matsalolin da ake fama da su a jihohin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng