Kwankwaso: An Fara Hasashen Wanda Tinubu ke So Ya Maye Gurbin Kashim a 2027
- Rahotanni sun ce Shugaba Bola Tinubu na duba yiwuwar maye gurbin Kashim Shettima gabanin zaɓen 2027 da ke ƙara ƙarato wa
- Wasu majiyoyi masu tushe a birnin Abuja sun shaida cewa Shugaban kasa da wasu manyan APC na harin Rabi'u Musa Kwankwaso
- Jam’iyyar APC na kallon Kwankwaso a matsayin jigo mai ƙarfi a Arewa, wanda zai taimaka wajen samun nasarar Tinubu a karo na biyu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Rahotanni sun fara nuna cewa shugaban kasa, Bola Tinubu na duba yiwuwar sauya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a zaben 2027.
Wata majiya mai tushe a Abuja ta ce hakan na daga cikin dalilan da shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje bai ambaci Shettima ba lokacin taron masu ruwa da tsaki a jihar Gombe.

Asali: Facebook
Majiyar da ta bayyana hakan ga jaridar Business Day, ta kara da cewa batun Kwankwaso ya samu karɓuwa sosai a tsakanin wasu jiga-jigan APC don ganin Tinubu ya samu nasara a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ana son maye gurbin Kashim da Kwankwaso
Majiyar ta ce ana ci gaba da tattaunawa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kuma an shaida cewa ya kai ziyara wajen shugaban kasa domin ƙara tattauna maganar.
Ta ƙara da cewa:
“Amma muna bukatar ya dawo cikin jam’iyyar tun da wuri.”
“Yana da abin da shugaban kasa da jam’iyyarmu ke bukata domin samun cikakken nasara a sake zaɓe na Bola Tinubu.”
Tinubu: APC ta gano muhimmancin Kwankwaso
Majiyar ta ƙara bayyana cewa APC ta gano Kwankwaso na da matuƙar amfani saboda ƙwarewarsa da gagarumin farin jini da ya ke da shi a Arewacin Najeriya.
Kwankwaso ya taba zama gwamnan Jihar Kano daga 1999 zuwa 2003 da kuma daga 2011 zuwa 2015, sannan yanzu haka shi ne jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa.

Asali: Facebook
Ya kuma rike mukamin Ministan Tsaro a zamanin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, yayin da ya ke jagorantar miliyoyin 'yan Kwankwasiyya. Shugaban na NNPP, wanda ake kallon sa a matsayin jagoran siyasar Kano, ya kuma taba zama Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya daga 2015 zuwa 2019.
Ana ganin Kwankwaso na da muhimmanci wajen taimakawa shugaban kasa wajen ƙarfafa APC a Kano da sauran jihohin Arewa maso Yamma. A zaben shugaban kasa na 2023, jam’iyyar NNPP ta su Kwankwaso ta zo ta huɗu a jerin waɗanda suka fi samun ƙuri’a a Najeriya.
Hanzari ba gudu ba
Ko da yake ana ta rade-radin cewa shugaban kasa Bola Tinubu na nagen Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya maye gurbin Kashim Shettima a zaben 2027, har yanzu ba a taba jin ya fito fili ya ce zai koma jam’iyyar APC ba.
Kwankwaso, wanda shi ne jagoran NNPP na ƙasa, bai taɓa nuna wata sha’awa ko niyya ta sauya sheka zuwa APC ba – jam’iyyar da ya sha suka a baya kuma da ya fice daga cikinta sakamakon sabani da Abdullahi Umar Ganduje, shugaban APC na yanzu.
Idan Kwankwaso ya koma APC, hakan na iya haifar da matsala ta cikin gida musamman ma ga Ganduje, wanda ke da tarihi na rikici da Kwankwaso tun daga lokacin da suka raba hanya a siyasar Kano.
Ganduje dai bai jin daɗin Kwankwasiyya da tasirinta a Kano, kuma yana da wuya ya marawa sauya-shekar tsohon gwamnan baya.
Wannan dalili ya sa har yanzu ba a kai ga samun sahihin matsayi daga jam’iyyar APC ko daga Kwankwaso kan wannan batu ba.
Sauya sheka irin wannan za ta buƙaci lissafi mai zurfi, duba da tasirin da zai iya yi wa shugabancin jam’iyyar da makomar siyasar Kano.
Wamakko ya magantu kan neman wurin Kashim
A baya, mun wallafa cewa Sanatan Sokoto ta Arewa a majalisar dattawa, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya nesanta kansa daga neman kujerar mataimakin shugaban ƙasa a 2027.
Wamakko, wanda kuma tsohon gwamnan Jihar Sakkwato ne, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Abdullah El-Kurebe, ya fitar a ranar Lahadi.
Sanatan ya ce bai yi wata magana a bainar jama’a ko a ɓoye da ke nuni da cewa yana da sha’awar tsayawa takara ko ta mataimakin shugaban ƙasa ko wani muƙamin siyasa a 2027 ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng