Wamakko Na Neman Maye Gurbin Shettima a 2027? An Ji Gaskiyar Zance

Wamakko Na Neman Maye Gurbin Shettima a 2027? An Ji Gaskiyar Zance

  • Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi martani kan batun cewa yana da burin zama mataimakin shugaban ƙasa a 2027
  • Tsohon gwamnan Sokoto ya musanta cewa yana da niyyar maye gurbin Kashim Shettima a babban zaɓen 2027 da ake tunkara
  • Sanatan ya nuna ya maida hankalinsa ne wajen kawo abubuwan ci gaba ga mutanen da yake wakilta a majalisar dattawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa, Aliyu Wamakko, ya yi magana kan batun cewa yana burin zama mataimakin shugaban ƙasa a 2027.

Sanata Aliyu Wamakko ya nesanta kansa daga rahotannin da ke danganta shi da wani ƙuduri na zama mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027 da ake tunkara.

Wamakko ya musanta neman kujerar Shettima
Wamakko ya ce bai da burin maye gurbin Shettima Hoto: Aliyu Magatakarda Wamakko, Kashim Shettima
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, wadda mai magana da yawun bakinsa Abdullah el-Kurebe ya sanyawa hannu, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Wamakko ya musanta neman kujerar Shettima

Tsohon gwamnan na jihar Sokoto kuma Sarkin Yamman Sokoto, ya bayyana cewa iƙirarin ƙarya ne, ba da izininsa aka fitar da shi ba, kuma yana da nufin ɓata siyasarsa ne kawai.

Wannan martani ya biyo bayan wata sanarwa da aka danganta ga shugaban ƙaramar hukumar Kebbe, Abdullahi Yerima.

Wamakko ya musanta yin wata magana a bainar jama’a ko a sirrance da ke nuna yana da niyyar tsayawa takarar kujerar mataimakin shugaban ƙasa ko wani muƙamin siyasa makamancin hakan a zaɓen 2027.

Kujerar Shettima ta jawo cece-kuce a jam'iyyar APC

Jam’iyyar APC na fama da rikici a kan makomar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a yayin da ake shirye-shiryen zaɓen 2027.

Kwanan nan, wani taron shugabannin jam’iyyar daga Arewa maso Gabas ya rikiɗe zuwa rikici bayan da aka nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu domin zaɓen 2027 ba tare da ambaton Shettima ba.

Tun daga lokacin, jita-jita ta bazu cewa yankin Arewa maso Yamma na shirin fitowa da ɗan takarar da zai maye gurbin Shettima a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Fadar shugaban ƙasa ta musanta jita-jitar cewa akwai saɓani tsakanin Tinubu da Shettima, tana mai jaddada cewa shugaban ƙasa ne zai zaɓi abokin takararsa bayan ya karɓi tikitin jam’iyya a babban taronta.

Me Wamakko ya ce kan maye gurbin Shettima

Da yake nesanta kansa daga duk wani yunƙuri da ya shafi maye gurbin Shettima, Wamakko ya jaddada cewa bai taɓa nuna sha’awar hakan ba, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Wamakko ya karyata batun neman kujerar Shettima a 2027
Wamakko ya ce bai da burin neman kujerar Shettima Hoto: Aliyu Magatakarda Wamakko
Asali: Facebook
“Muna so mu bayyana a fili cewa Sanata Wamakko bai taɓa, a kowane lokaci, a fili ko a sirrance, nuna sha’awa ko niyyar tsayawa takarar kujerar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba, ko shiga kowane irin tsarin siyasa makamancin hakan."
“Duk wani zargi ko iƙirari dangane da hakan ƙarya ne, ba shi da tushe, kuma rashin ɗa’a ne kwata-kwata."

- Abdallah el-Kurebe

Tsohon gwamnan ya kuma siffanta kalaman da Abdullahi Yerima ya yi a matsayin abin da ya nuna rashin ƙwarewa da ƙoƙarin yaudara, da jefa sunansa cikin jita-jita marasa tushe a siyasa.

Sanarwar ta buƙaci shugaban ƙaramar hukumar Kebbe da ya janye kalamansa cikin gaggawa, tare da bayar da haƙuri a fili ga sanatan da kuma iyalansa.

“Ya zama tilas a ajiye a tarihi cewa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko na ci gaba da mayar da hankali wajen yi wa al’ummar jihar Sokoto da ƙasa baki ɗaya hidima ta hanyar shugabanci nagari da ƙwarewar siyasa."
"Kuma bai kamata a ja shi cikin ƙagaggun labaran da wasu ke ƙirƙira domin cika burinsu na ƙashin kai ba."

- Abdallah el-Kurebe

Jigon APC ya magantu kan saɓanin Tinubu, Shettima

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani babban ƙusa a jam'iyyar APC, Ismaeel Ahmed ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa akwai saɓani tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima.

Jigon na APC ya bayyana cewa babu wani saɓani da ke tsakaninsu illa kawai mutane kawai ke ƙoƙarin ƙirƙirarsa.

Hakazalika ya yi watsi da batun cewa ana shirin maye gurbin Kashim Shettima gabanin zaɓen shekarar 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta [email protected]

OSZAR »