Ramalan Yero, Shehu Sani da Jerin 'Yan Adawan da Uba Sani Ya Jawo APC a Kaduna
Kaduna - Jihar Kaduna, wacce ta kasance jigo a siyasar Arewa maso Yammacin Najeriya, na fuskantar sauya shekar manyan 'yan siyasa daga jam'iyyu daban daban.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ana ganin cewa Gwamna Uba Sani ne ke rike da sitiyarin motar sauye-sauyen da ake samu, kuma tasirinsa da kwarewarsa ya jawo 'yan PDP da dama sun koma APC.

Asali: Twitter
Daga tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, har zuwa irin su Shehu Sani, Gwamna Uba Sani ya yi nasarar cika APC da kusoshin 'yan siyasar jihar.
Wannan nasara da Uba Sani ya samu, ta sanya jam'iyyar APC ta kara yin karfi a Kaduna yayin da ta bar jam'iyyun adawa suna tangal-tangal gabanin zaben 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Uba Sani - Masarrafin siyasar Kaduna
Kwarewar Gwamna Uba Sani ta jan ra'ayin manyan 'yan adawa zuwa APC ya samo asali daga kwarewarsa a Muki, da kuma sanin makamar siyasar.
Duk da cewa ya sha da-kyar a zaben 2023, inda ya lashe zaben gwamnan Kaduna da tazarar kuri'u 11,000 kacal tsakaninsa da Isa Ashiru na PDP, ana ganin Uba Sai ya fifita hadin kai da ci gaban jihar a mulkinsa.
Gwamnatinsa ta mayar da hankali kan gina abubuwan more rayuwa, samar da ilimi, tsaro da bunkasa matasa, ba tare da la'akari da matsayin siyasa ba.
A wani babban taro da aka gudanar a ranar 16 ga Fabrairu, 2025, Uba Sani ya karbi manyan 'yan siyasa 50 zuwa APC, ciki har da Shehu Sani, Mukhtar Ramalan Yero, Sanata Suleiman Hunkuyi, Sani Sha'aban, da dai sauransu.
Yayin da ya ke ba su tabbacin samun adalci da damarmaki a APC, Uba Sani ya shaida wa su Shehu Sani cewa:
"Muna kallon wadanda suka shiga APC a yau da wadanda suka kafa jam'iyyar shekaru 10 da suka wuce a matsayin abu daya, matsayinsu daya a wajenmu."

Asali: Facebook
Sauya shekar Namadi Sambo
A ranar 18 ga watan Yuni, 2025 ne jaridar The Guardian da wasu jaridu suka ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya fice daga PDP zuwa APC.
Namadi Sambo wanda ya yi mataimakin shugaban kasa a zamanin Goodluck Jonathan daga 2010 zuwa 2015 da kuma gwamnan Kaduna daga 2007 zuwa 2010, ya samu tarba daga Gwamna Uba Sani a gidan gwamnati na Sir Kashim Ibrahim.
Sauya shekarsa ta girgiza PDP, wacce dama take cikin rikici. Ana ganin komawarsa APC zai kara wa jam'iyya mai mulkin karfi a Arewacin Najeriya a 2027.
Duk da cewa Namadi Sambo bai bayyana dalilin sauya shekarsa a fili ba, amma masana na ganin cewa rikicin PDP da ci gaba da Uba Sani ya kawo Kaduna ne ya sa shi komawa APC.
To sai dai kuma, mun ruwaito cewa mai ba Namadi Sambo shawara kan kafofin sadarwa, Umar Sani a ranar 19 ga Yuni, 2025 ya karyata wannan rahoto.
Umar Sani ya ce labarin sauya shekar Namadi Sambo karya ce tsagoronta, amma hakan bai hana fitattun kafofin watsa labarai irin su Punch tabbatar da labarin ba.

Asali: Facebook
Yadda Sanata Shehu Sani ya koma APC
Sanata Shehu Sani ya sauya sheka daga PDP zuwa APC a Fabrairun 2025, wanda ake ganin ya kara tabbatar da dabarun siyasar Gwamna Uba Sani.
Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, ya shiga takun saka da APC a baya.
Wanda aka zaba zuwa majalisar dattawa a 2015, lokacin da shi ma tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya ci zabe, ya bar APC a 2018, bayan samun sabani da El-Rufai.
Ya shiga jam'iyyar APC, inda ya samu tikitin kujerar sanata, amma ya sha kasa a hannun Uba Sani a 2019. Ana ganin sasancin da Uba Sani ya nema ne ya sa Shehu Sani ya koma APC.
A wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), Shehu Sani ya ce zai goyi bayan tazarcen Uba Sani a 2027, saboda ci gaban tsaro da ababen more rayuwa da aka samu.
"Tun da Uba Sani ya hau mulki, abubuwa suka canja, aka samu ci gaba sosai. Mun rage jin sace-sacen mutane a Kaduna."
- Shehu Sani.
Sauya shekar da Sanata Shehu Sani ya yi ta bar babban gibi a PDP, wanda aka ce ya kara jefa jam'iyyar a mawuyacin hali, na rashin kusoshinta a Kaduna.

Asali: Facebook
Sauya shekar Mukhtar Raman Yero
Mukhtar Ramalan Yero, tsohon gwamnan jihar Kaduna, kuma abokin kamanceceniyar Namadi Sambo, shi ma ya fice daga PDP zuwa APC, kamar yadda muka ruwaito.
Ramalan Yero, wanda ya mulki Kaduna daga 2012 zuwa 2015, ya sauya sheka zuwa PDP a watan Satumbar 2023 tare da Sanata Danjuma Laa da tsohon sakataren tsare-tsare, Abubakar Mustapha.
Sauya shekarsa zuwa APC, la'akari da babbar alakar da ke tsakaninsa da Namadi Sambo da kuma PDPn Arewa, ya zama babban koma baya ga 'yan adawa.
A wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Zaria a ranar 16 ga Yuni, 2025, Ramalan Yero ya nemi a gudanar da yakin zabe na gida-gida domin APC ta yi nasara a 2027.
Tasirin sauya shekar Sani Sidi ga 'yan adawa
Muhammad Sani Sidi, wani na hannun daman Namadi Sambo, kuma tsoron shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ya sauya sheka zuwa APC a ranar 18 ga Yuni, 2025.
Ya sauya shekar ne tare da dubunnan magoya bayansa a wani babban taro da aka gudanar a kasuwar duniya da ke Kaduna, inji rahoton The Nation.
An bayyana taron, wanda ya samu jagorancin Gwamna Uba Sani, kuma wanda Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya halarta a matsayin 'babban sauyin siyasa a Kaduna."
Muhammadu Sidi ya ce ci gaban da jam'iyyar PDP ta samu da kuma namijin kokarin Uba Sani a fuskar gine-gine, ilii da tsaro, su ne suka ja ra'ayinsa ya koma APC.
Tasirin sauya shekar 'yan siyasa ga zaben 2027
Aba ganin Nasarar Uba Sani ta jawo fitattun 'yan siyasa irinsu, Sambo, Shehu Sani, Yero da Sidi za ta hana 'yan adawa rawar gaban hantsi a 2027.
Kaduna, wacce ke taka rawa a siyasar Najeriya, yanzu tana karkashin APC, yayin da PDP ta afka cikin rikici da kuma rasa jiga-jiganta a jihar.
Gwamnatin Uba Sani, da ta kaddamar da sama da sababbin tituna 62, makarantun sakandare 60 da raba taki kyauta ga manoma, ya karya karya tasirin 'yan adawa.
Sai dai kuma, Sanata Lawal Usman na PDP ya karyata cewa jam'iyyarsa ta rushe a Kaduna, yana mai cewa APC ta riga ta rasa kima a idon jama'a.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Sanata Lawal ya ce APC ta yo hayar jama'a ne kawai suka cika wurin taronta, amma ba wai don suna son jam'iyyar ba.
'Ba girin girin ba ta yi mai' - Kwamared Ya'u
Wani matashin dan jam'iyyar PDP a Kaduna, Kwamared Ya'u Shareef, ya ce ba sauya sheka ne ke yanke hukunci kan makomar siyasar Kaduna ba.
Kwamared Ya'u ya yi ikirarin cewa dukkanin wadanda suka koma APC, irinsu Shehu Sani, ba su tsinanawa PDP komai ba a 2023, amma duk da hakan jam'iyyar ta kusa ba APC kashi.
"Ka san mu har gobe mun yarda cewa muna muka ci zabe a Kaduna, amma babu yadda muka iya, mun dauki kaddara. Ina so ka sani cewa, PDP tana da karfi fiye da ya tunani a Kaduna.
"Wai dan su Shehu Sani, ko Ramalan Yero sun koma APC ba shi zai daga mana hankali ba, ai siyasa yawan jama'a ne, yawan masu kada kuri'a, ba wai wasu tsirarun 'yan siyasa ba.
"Ina mai tabbatar maka cewa, yanzu da APC ta rasa Malam Nasir El-Rufai to kashinta ya bushe. Babu inda Uba Sani zai je a 2027. Dama ai Malam ne ya tsaya masa a 2023, to yanzu kuma sun yi hannun riga."
Uba Sani ya nada sababbin kwamishinoni
A wani labarin, mun ruwaito cewa, mai girma Gwamna Uba Sani ya naɗa sabbin kwamishinoni a jihar Kaduna domin gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.
Gwamna Uba Sani ya naɗa Farfesa Abubakar Sambo a matsayin Kwamishinan Ilimi, yayin da aka sauya ma'aikatar Farfesa Sani Bello.
Gwamnan ya bayyana cewa yana da yakin kwamishinonin za su kawo sauyi mai ma'ana a ma'aikatunsu tare da samar da hanyoyin warware matsalolin da jihar ke fuskanta.
Asali: Legit.ng