Abubuwan Sani game da Ƴan Takara 4 na Sahun Gaba a Zaɓen Gwamnan Anambra 2025

Abubuwan Sani game da Ƴan Takara 4 na Sahun Gaba a Zaɓen Gwamnan Anambra 2025

Anambra - Bayan Hukumar Zaɓe (INEC) ta ba da damar fara kamfen, jam’iyyu da ‘yan takararsu sun ƙara ƙaimi a shirin tunkarar zaben gwamna a Anambra.

Hukumar INEC ta shirya gudanar da zaɓen gwamnan Anambra a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2025.

Yan takarar da ke shirin fafatawa a zaben gwamnan Anambra.
Gwamna Soludo zai kara da ƴan takarar APC, PDP da LP a zaben gwamnan Anambara 2025 Hoto: Charles Chikwuma Soludo, Nicholas Ukachukwu
Asali: Facebook

INEC ta fitar da sunayen ƴan takara da jam'iyyu

A wata sanarwa da ta wallafa a shafin X, INEC ta fitar da jerin sunayen ƴan takara na ƙarshe, waɗanda suka cancanci fafatawa a zaɓen gwamnan da ke tafe.

Hukumar INEC ta kuma bayyana cewa jam’iyyu 16 ne suka cika sharudda domin shiga zaɓen Anambra da za a yi a wannan shekara ta 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Jam'iyyar APGA ce ke mulki a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya kuma ta jima tana jagorantar jihar duk da ƙoƙarin jam'iyyu na karɓe mulki.

Jerin ƴan takarar gwamma 4 a Anambra

Masu lura da al’amura sun ce wannan zaɓe zai kasance mai kayatarwa, musamman saboda gwamna mai ci, Farfesa Charles Soludo, na neman wa’adi na biyu.

Legit Hausa ta tattaro muku manyan ƴan takara huɗu na sahun gaba, waɗanda ake ganin ɗayansu ne zai lashe zaɓen gwamnan Anambra a watan Nuwamba. Ga su kamar haka:

1. Charles Chukwuma Solụdo (APGA)

Shi ne gwamnan jihar Anambra mai ci a halin yanzu, kuma yana neman wa’adi na biyu a ƙarƙashin jam’iyyar APGA.

Gwamna Soludo ya rike kujerar gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma shugaban kwamitin daraktocin bankin daga 2004 zuwa 2009.

An haife shi a ranar 28 ga Yuli, 1960. Soludo ya lashe zaɓen gwamnan Anambra karo na farko a shekarar 2021 inda ya gaji, Willie Obiano.

Gwamna Soludo na jihar Anambra.
Gwamna Anambra. Farfesa Charles Soludo yana neman tazarce a zaɓen 2025 Hoto: Charles Chukwuma Soludo
Asali: Twitter

Wasu masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa Soludo na iya sake lashe zaɓen, duba da damar da yake da ita, karfin mulki da alaƙarsa da manyan masu faɗa aji a jihar.

A 'yan kwanakin nan, Gwamna Soludo ya nuna goyon baya ga tazarcen Shugaba Tinubu a zaɓen 2027 duk da yana cikin jam'iyyar hamayya.

Masana harkokin siyasa sun ce wannan goyon bayan na nuni da cewa Tinubu da Soludo na da wata yarjejeniya dangane da zaɓen gwamnan Anambra mai zuwa.

Sai dai Daraktan Yaɗa Labarai na jam’iyyar APC, Bala Ibrahim, ya shaida wa Daily Trust ta wayar tarho cewa ba Tinubu ne ya marawa Gwamna Soludo baya ba.

“Dangane da wannan goyon baya, gwamnan ne kawai ya nuna goyon baya ga shugaban ƙasa, ba wai Tinubu ne ya goyi bayan gwamnan ba.
"Wannan wani abu ne daban. A siyasa, kowace jam’iyya na da nata ɗan takarar shugaban ƙasa, amma wannan goyon baya bai haɗa da zaɓen gwamna ba

2. Prince Nicholas Ukachukwu (APC)

Prince Nicholas Ukachukwu, shi ne ɗan takarar APC a zaɓen da ke tafe, tarihin siyasarsa cike yake da sauye-sauyen jam'iyyu daga wannan zuwa wannan duk a ƙoƙarin neman mulki.

Ɗan takarar wanda aka fi sani da Ikukuoma, ɗan kasuwa ne kuma ɗan siyasa, wanda ya shafe shekaru yana aiki a fannoni kamar harkar gidaje, mai da iskar gas, da kuma hidimar jama'a.

Dan takarar APC a zaben Anambra, Nicholas Kachukwu.
Zaben Anambra: Nicholas Kachukwu na da kalubale a gabansa Hoto: Nicholas Kachukwu
Asali: Facebook

An haife shi a ranar 20 ga watan Maris, 1969. Ya samu nasarar zama mamba mai wakiltar mazabar Bwari/Abuja Municipal a Majalisar Wakilai a inuwar jam’iyyar PDP daga 1999 zuwa 2003.

Daga baya Ukachukwu ya fice daga PDP, ya tsaya takarar Sanata a yankin Anambra ta Kudu a 2003 ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, amma bai yi nasara ba.

Kafin zaɓen 2007, ya koma PDP ya kuma tsaya takara don komawa Majalisar Wakilai, amma shi ma bai yi nasara ba.

A 2013, ya sake gwada sa’a a zaɓen gwamnan jihar Anambra a ƙarƙashin jam’iyyar APGA, amma bai samu nasara ba.

Ukachukwu ya kuma tsayawa takarar Sanata a 2019 don wakiltar Anambra ta Kudu a inuwar jam'iyyar APC, amma ya sha kaye a hannun Sanata Ifeanyi Ubah, wanda ya rasu a bara.

Shi kaɗai ne ɗan takarar da ke da tarihin sauya jam’iyya sau da dama don neman kujerar siyasa. Masana siyasa na ganin irin wannan tarihi zai sa jam’iyyar APC ta fuskanci ƙalubale wajen tallata shi ga masu zaɓe.

3. Jude Ezenwafor (PDP)

Jude Ezenwafor, ɗan kasuwa mai harkar gine-gine kuma ɗan takarar PDP a zaɓen ranar 8 ga Nuwamba, 2025, kamar yadda The Cable ta kawo.

Ezenwafor, wanda aka haife shi a ranar 21 ga watan Yuli, 1980, ya jima a jam'iyyar APGA inda ga shiga zaɓen fidda gwani a 2021 amma bai yi nasara ba, daga bisani ya koma PDP.

Dan takarar PDP a zaben Anambra, Jude Ezenwafor.
Ana ganin rikicin PDP zai iya jawo wa Jude Ezenwafor babban cikas a zaɓen Anambra Hoto: Official PDP Nigeria
Asali: Facebook

Ya samu nasarar zama ɗan takarar PDP ne ba tare da hamayya ba, bayan ya sayi fam ɗin takara Naira miliyan 40 kuma ya samu ƙuri'u 853 a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a Awka.

Sai dai masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa zai shiga zaɓe da babbar matsala duba da rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar PDP a matakin ƙasa.

4. George Moghalu (LP)

Moghalu shi ne Auditan APC na ƙasa na farko kuma, ya kasance mamba a kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC). Ana haife shi a ranar 10 ga watan Disamba, 1962.

Ya nemi tikitin APC don takarar gwamna a 2021, amma ya sha ƙasa. Ya garzaya kotu yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen fidda gwani, kuma ya yi nasara a kan jam’iyyar.

George Moghalu.
Tsohon Auditan APC ya lashe tikitin takarar gwamnan Anambra a inuwar LP Hoto: @NGLabour
Asali: Twitter

Kotu ta umarci INEC da ta goge sunan Andy Uba, wanda aka bayyana a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen fidda gwani.

Sai dai, saboda wasu rikice-rikicen siyasa, dabaru da kuma ƙarancin lokaci, daga bisani aka naɗa Moghalu a matsayin Manajan Darakta na Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa (NIWA).

A watan Agusta na bara, ya fice daga APC, sannan a watan Oktoba, ya koma LP, inda ya nemi tikitin takarar gwamna kuma ya lashe zaɓen fidda gwani, kamar yadda jam'iyyar ta wallafa a shafin X.

Jam'iyyu za su biya kudin kamfe a Anambra

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyun siyasa 16 a Anambra za su biya N800m don samun izinin gudanar da yakin neman zabe da kafe allunan tallata 'yan takara.

Gwamnatin Anambra ta bukaci kowace jam'iyyar siyasa ta biya N50m kafin a ba ta izinin kafe allunan yaƙin neman zaɓenta.

Tuni wannan sabon umarnin na gwamnatin Anambra ya haifar da cece-kuce a jihar, yayin da jam'iyyar LP da APC suka yi watsi da umarnin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »