Jam'iyyar PDP Ta Sake Rikicewa da Namadi Sambo Ya Watsar da Ita Zuwa APC
- Siyasar Arewa na sauyawa yayin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo, ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki
- Gwamna Uba Sani na Kaduna ne ya karɓi Sambo a hukumance a Fadar Gwamnatin Sir Kashim Ibrahim ranar Laraba, 18 ga Yuni, 2025
- Sauyin sheƙar da ake gani daga PDP zuwa APC na da nasaba da rikicin cikin gida da rashin daidaito a shugabancin jam’iyyar adawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Siyasar Najeriya musamman a Arewacin kasar na sake daukar sabon salo gabanin zaben shekarar 2027 da ke tafe.
Hakan bai rasa nasaba da yadda manya kuma jiga-jigan yan siyasa a yankin ke sauya sheka zuwa APC da kuma shirin yan adawa da ke kokarin yin kawance kan zaben.

Asali: Facebook
Namadi Sambo ya koma jam'iyyar APC mai mulki
Rahoton Arise News ya tabbatar da cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Mohammed Namadi Sambo ya koma APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
A cikin wasu hotuna da ake yadawa, an gano Namadi Sambo da Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna.
Hakan shi ke nuna alamar cewa Uba Sani ne ya karbi tsohon gwamnan jihar zuwa APC, kamar yadda rahoton The Guardian ya ruwaito.
Namadi Sambo ya taɓa zama Mataimakin Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin shugabancin Goodluck Jonathan daga 2010 zuwa 2015.

Asali: Facebook
Wanene ya karbi Namadi Sambo a APC?
An karɓe shi a hukumance cikin jam’iyyar APC a ranar Laraba ta hannun Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani.
Taron ya gudana ne a yau Laraba 18 ga watan Yunin 2025 a Fadar Gwamnatin Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna.
Duk da cewa Namadi Sambo bai fitar da wata sanarwa ba tukuna, masu fashin bakin siyasa na cewa wannan mataki na iya tayar da kura.
Masanan siyasa suka ce za a iya samun matsala tsakanin masu karfin fada a ji a Kaduna tare da haifar da tambayoyi kan kawance kafin zaben 2027.
Yadda PDP ta yi rashin jiga-jiganta a Arewa
Sauya shekar Namadi Sambo daga PDP zuwa APC ya zo ne a daidai lokacin da manyan ‘yan siyasa ke barin PDP.
Daga cikin wadanda suka bar PDP har da sanatoci, ‘yan majalisar tarayya da shugabannin jihohi, wanda suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar mai mulki ta APC cikin ‘yan watannin nan.
Ana danganta wannan sauyin sheƙa da rikice-rikicen cikin gida a PDP da kuma rashin warware matsalolin shugabanci da jam’iyyar ke fama da su.
Yayan Namadi Sambo ya yi bankwana da duniya
Mun ba ku labarin cewa dan uwan tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriya, Mohammed Namadi Sambo ya rasu yana da shekaru 82 a duniya.
Marigayiyin ya kasance yayan Namadi Sambo mai suna Alhaji Sulaiman Sambo, ya rasu bayan fama da jinya kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Mutane da dama da suka halarci janazar sun yaba da irin halayen dattaku da yake da shi da gudunmawa da ya bayar ga al'umma lokacin da yake raye.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng