Kamar Jonathan a 2015, SDP Ta Hango Faduwar APC a Zaben 2027

Kamar Jonathan a 2015, SDP Ta Hango Faduwar APC a Zaben 2027

  • Shugaban jam’iyyar SDP na jihar Ebonyi, Dr Kingsley Agbor, ya bayyana cewa jam’iyyarsu na ci gaba da kara karfi domin fuskantar APC a 2027
  • Ya ce gwamnatin APC na fuskantar rashin amincewa daga jama’a saboda matsin tattalin arziki da gazawar gwamnatin kasar a manyan fannoni
  • Agbor ya ce APC za ta fadi a 2027 kamar yadda PDP ta sha kaye a 2015, tare da bayyana SDP a matsayin amintacciyar madogara ga 'yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ebonyi - Shugaban SDP a jihar Ebonyi, Dr Kingsley Agbor, ya bayyana cewa jam’iyyarsa na kulla dabarun domin fatattakar jam’iyyar APC a 2027.

A cewarsa, matsin rayuwa da gazawar gwamnati sun jefa 'yan Najeriya cikin bacin rai, kuma hakan zai ba su dama su nuna fushinsu a zabe mai zuwa.

Shugaban SPD ya ce APC za ta fadi a 2027
Shugaban SPD ya ce APC za ta fadi a 2027. Hoto: Bayo Onanuga|Shehu Musa Gabam
Asali: Twitter

Agbor ya bayyana haka ne yayin wata hira da jaridar Punch, inda ya bayyana cewa kamar yadda PDP ta fadi a 2015, hakan ma zai faru da APC idan lokaci ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

"SDP na shirye sosai a jihar Ebonyi" - Agbor

A matakin jiha, Dr Kingsley Agbor ya musanta zargin da ke cewa jam’iyyarsa ba ta da tasiri a Ebonyi.

Ya ce:

“Muna aiki tare, muna kara karfi a hankali. Rana tsaka za a fahimci irin irin nasarar da muka cimma.”

Ya ce kasancewar jam’iyyar ba riko da madafun iko a gwamnatance take ba ya sa suke amfani da dabaru da hangen nesa don shiryawa 2027

“Za mu bai wa mutane mamaki,”

In ji shi.

SDP ta ce dimokuradiyya ta ci baya a Najeriya

A zantawar da aka yi da shi, Agbor ya ce dimokuraɗiyyar Najeriya ba ta kai matsayin da za a iya kiran gwamnati ta jama’a ba a kasar nan.

A cewar shi:

“Ina ruwan jama’a da gwamnati? Gidaje nawa ne ke da ruwa ko wutar lantarki? Wannan ba cigaba ba ne,”

Kwanan nan aka yi bikin ranar damukaradiyya domin tunawa da nasarar mulkin farar hula da aka shafe shekaru kusan 26 ana yi a yau.

Jam'iyyar APC za ta sha kaye a 2027 inji Agbor

A cewarsa, zaben 2027 ba zai kasance tsakanin PDP da APC ba, sai dai tsakanin Najeriya da jam'iyyar APC.

Dangane da kalaman Ministan Ayyuka, David Umahi, da ya ce masu adawa da Shugaba Tinubu ba su da kima, Agbor ya ce irin wannan raini ya sa PDP ta fadi a 2015.

El-Rufa'i na ganawa da Atiku.
Jigon SDP, El-Rufa'i na ganawa da Atiku. Hoto: Paul Ibe
Asali: Twitter

Shugaban SDP ya ce:

“Na tuna abin da El-Rufai ya fada lokacin da suke hada APC, cewa ‘ba za ku iya sauke gwamnati mai ci ba’. Amma sun yi. Hakan ma zai faru a 2027.

Rikicin siyasa: PDP ta yi wa APC dariya

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta rama bakar magana da shugaba Bola Tinubu ya fada mata a ranar dimokuradiyya.

A ranar 12 ga Yuni da aka yi bikin ranar dimokuradiyya Bola Tinubu ya ce yana jin dadin yadda rikici ke karuwa a PDP.

Jam'iyyar PDP ta yi martani wa Bola Tinubu da APC bayan bullar rikici a taron jam'iyyar APC na Arewa maso Gabas da aka yi a Gombe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »