PDP Ta Rama Dariyar da Tinubu Ya Mata bayan an Farmaki Ganduje a Gombe

PDP Ta Rama Dariyar da Tinubu Ya Mata bayan an Farmaki Ganduje a Gombe

  • Jam’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da rikicin da ya kunno kai a taron masu ruwa da tsaki na APC na Arewa maso Gabas da aka gudanar a Jihar Gombe
  • PDP ta bayyana cewa rikicin ya bayyana rashin jituwa da yarda tsakanin manyan shugabannin jam’iyyar APC mai rike da mulkin Najeriya
  • Ta ce duk da cewa suna jin dadin yadda rikicin APC ke bayyane, su a PDP za su ci gaba da bin tafarkin siyasa mai tsafta ba tare da tashin hankali ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - PDP ta bayyana damuwa tare da suka ga jam’iyyar APC kan rikicin da ya bulla a taron jam’iyyar a shiyyar Arewa maso Gabas da aka gudanar a Gombe.

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa hakan alama ce ta yadda jam’iyya mai-ci ke fama da rikice-rikicen cikin gida gabanin zaben 2027.

PDP ta ce ta ji dadin rikicin da ya bulla a APC
PDP ta ce ta ji dadin rikicin da ya bulla a APC. Hoto: Bayo Onanuga|Official PDP
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban matasa na kasa a PDP, Timothy Osadolor ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Vanguard a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Timothy Osadolor ya ce PDP ba za ta lamunci siyasar tashin hankali ba, kuma ba za ta tsaya kallon APC tana yada rikici ba.

PDP ta caccaki shugabannin jam'iyyar APC

Osadolor ya ce rikicin ya samo asali ne daga rashin yarda tsakanin gwamnonin Arewa maso Gabas kan wanda zai maye gurbin Kashim Shettima idan ba a sake tsayar da shi ba a zaben 2027.

Ya ce akwai rade-radin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai sake daukar Shettima a matsayin mataimakinsa ba a zaben da ke tafe, lamarin da ya kara jefa APC cikin rudani.

Osadolor ya ce:

“Shin ya kuke tsammanin zaman lafiya idan shugabannin jam’iyyar na wulakanta ‘yan uwansu da suka fi cancanta a yankinsu?”

Jam'iyyar PDP ta rungumi siyasa mai tsafta

Duk da cewa PDP na jin dadin rikicin da APC ke ciki, Osadolor ya bayyana cewa jam’iyyarsu ta PDP ba za ta taɓa yarda da siyasar tashin hankali ba.

Ya ce:

“Muna son duniya ta san cewa siyasa ba tashin hankali ba ce.
Ba za mu lamunci yadda APC ke kokarin nuna wa matasa da sauran al’umma cewa tashin hankali wani bangare ne na siyasa ba.”

Ya kuma bukaci shugabannin APC da su ba da kyakkyawan misali ga matasan Najeriya da sauran masu sa ido.

PDP ta ce APC na son kawo rikici a siyasa.
PDP ta ce APC na son kawo rikici a siyasar Najeriya. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

'Jam’iyyar APC na kara yin barna da kanta' – PDP

Osadolor ya ce ko da yake PDP ba za ta tsoma baki a cikin rikicin APC ba, su na kallon hakan a matsayin dama domin nuna kwazon su wajen tafiyar da siyasa cikin lumana.

Ya ce:

“Muna farin cikin yadda suke nuna rudaninsu su a fili, kuma muna fatan rudanin nasu ya dore,”

Legit ta tattauna da dan APC a Gombe

Wani matashi dan APC a jihar Gombe, Aminu Isa ya ce abin da ya faru a Gombe rashin jituwa ne ba rikicin cikin gida ba.

Aminu ya ce:

"Idan ka lura, shugabannin APC ba su adawa da takarar Shettima. Saboda haka ba wai rikici ba ne, kawai wasu ne ba su fahimci yanayin ba."
"Da a ce akwai masu adawa da takarar ne za a ce ana rikici."

Ministan Buhari ya gargadi APC kan Shettima

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon minista a gwamnatin tarayya, Adebayo Shittu ya gargadi APC kan rade radin sauya Kashim Shettima a 2027.

Adebayo Shittu ya ce yana da tabbas a kan cewa za a sami baraka a APC idan aka ajiye Kashim Shettima a zaben 2027.

Hakan na zuwa ne bayan an ba hamata iska a taron APC da ya gudana a Gombe kan rade radin ajiye Shettima a takarar zabe mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »