Ajiye Shettima a 2027: APC da Fadar Shugaban Kasa Sun Yi Magana

Ajiye Shettima a 2027: APC da Fadar Shugaban Kasa Sun Yi Magana

  • Rikici ya barke a taron shugabannin APC na Arewa maso Gabas a Gombe dangane da rade-radin cire Kashim Shettima daga matsayin mataimakin Bola Tinubu
  • An ruwaito cewa magoya bayan Shettima sun fusata lokacin da wasu shugabannin jam’iyyar suka gaza bayyana goyon bayansu ga takara tsakanin Bola Tinubu da Shettima
  • Wasu jiga-jigai sun yi barazanar komawa PDP idan aka yi watsi da Shettima, lamarin da ke nuna cewa APC na fuskantar barazana daga cikin gida a yankin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Yayin da zaɓen shekarar 2027 ke kara matsowa, wani sabon rikici ya kunno kai a cikin jam’iyyar APC.

An fara rikicin ne kan rade-radin da ke yawo cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai sauya mataimakinsa Kashim Shettima daga tikitin takararsa.

Abin da ke faruwa a APC kan takarar 2027
Fadar shugaban kasa ta ce bata san da maganar sauke Shettima a 2027 ba. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Punch ta tattauna da wasu 'yan APC bayan rade-radin ya haddasa hargitsi a wani taron shugabannin APC na Arewa maso Gabas da aka gudanar a Gombe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Taron da aka shirya domin jaddada goyon baya ga Tinubu a 2027 ya rikide zuwa rikici bayan wasu jiga-jigai sun gaza ambato Shettima a matsayin wanda za a ci gaba da tafiya da shi.

Wannan lamari ya fusata magoya bayan Shettima, inda aka ga wani dan jam’iyya yana dukan wani jigo da kujera.

Rikicin APC da aka yi a Gombe

A lokacin da mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa daga Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, ya gabatar da jawabi ba tare da ambaton Shettima ba, hakan ya tayar da ƙura.

Magoya bayan Shettima sun fara nuna fushi da hakan, musamman bayan shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya gaza ambaton Kashim a jawabinsa.

Bayan taron ya rikide, an fara jin kiraye-kirayen cewa:

“Babu Shettima, babu APC a Arewa maso Gabas.”

Wani jigon APC a jihar Adamawa ya ce sun sha alwashin komawa PDP a 2027 idan aka watsar da Shettima daga tikitin tazarce.

Shettima: Maganar APC da fadar shugaban kasa

Duk da hargitsin, wasu jiga-jigan jam’iyyar da kuma fadar shugaban kasa sun musanta rade-radin.

Mataimakin shugaban APC na Kudu maso Gabas, Dr Ijeoma Arodiogbu, ya bayyana cewa babu wata alama ko magana da ke nuna cewa Tinubu na da niyyar sauya mataimakinsa.

Shi ma mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Daniel Bwala, ya ce:

“Ban da masaniya kan batun."

A cewar Arodiogbu, wannan rade-radi kawai ƙoƙari ne na ɓata suna da rikita al’umma kafin lokacin siyasa ya kankama.

APC ta ce ba maganar sauke Shettima a 2027.
APC ta ce ba maganar ajiye Shettima a 2027. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Takarar tazarce da baraka a APC

Yayin da jam’iyyar APC ta riga ta bayyana Tinubu a matsayin ɗan takara tilo a 2027, ba a fayyace matsayin Shettima ba a hukumance.

Wannan lamari da ke tasowa daga Arewa maso Gabas na iya haifar da babbar barazana ga nasarar jam’iyyar a zaɓen mai zuwa.

Vanguard ta wallafa cewa ta samu rahoto a kan cewa gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ba ya goyon bayan tafiya da Shettima a 2027 dik da bai bayyana hakan ba.

Za a samawa Tinubu kuri'a miliyan 10

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen mai fada a ji a yankin Neja Delta da aka fi sani da Tompolo ya ce zai nemawa Bola Tinubu kuri'u a 2027.

Wata kungiya mai goyon bayan Bola Tinubu da ke karkashin Tompolo ce ta bayyana hakan a wani taro a ranar dimokuradiyya.

Kungiyar ta ce Tompolo zai bi gida gida a Najeriya domin wayar da kan mutane da tarawa Tinubu kuri'u da suka kai miliyan 10.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »