Taron Masu Ruwa da Tsakin APC Ya Rikice a Gombe, Jami'an Tsaro Sun Ɗauke Ganduje

Taron Masu Ruwa da Tsakin APC Ya Rikice a Gombe, Jami'an Tsaro Sun Ɗauke Ganduje

  • Taron shugabannin APC na Arewa maso Gabas a Gombe ya rikide, bayan ganawa kan goyon bayan zaben Bola Tinubu a 2027
  • Rigimar ta fara ne bayan an ƙi ambaton mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ba yayin goyon Tinubu
  • Daga bisani, Abdullahi Ganduje ma bai ambaci Shettima ba a jawabinsa, lamarin da ya haddasa rikici har aka rufe taron da wuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - An samu rikici a taron jiga-jigan APC na yankin Arewa maso Gabas a ranar Lahadi 15 ga watan Yunin 2025 a jihar Gombe.

Lamarin ya faru ne bayan da mataimakin shugaban jam’iyya na kasa a yankin, Kwamred Mustapha Salihu yake nuna goyon baya ga Bola Tinubu a 2027.

Taron APC kan Tinubu, Shettima ya koma rigima
Taron APC ya rikice kan goyon bayan Tinubu a Gombe. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

2027: Taron APC ya koma rigima a Gombe

Daily Trust ta ce Salihu ya ƙi ambaton sunan Kashim Shettima yayin da yake marawa Bola Tinubu baya don sake tsayawa takara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Taron wanda aka gudanar a Jihar Gombe, ya samu halartar kusan duka ministoci, ‘yan majalisa da gwamnonin jam’iyyar daga yankin.

Abdullahi Ganduje, Shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya jagoranci wasu manyan jiga-jigai zuwa wajen taron.

A lokacin da Salihu ya yi jawabi, ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu don ya zama dan takara daya tilo, amma bai ambaci Shettima ba.

Yadda taron ya rikice kan goyon bayan Tinubu

Da ya kammala jawabin nasa, wakilan da ke taron suka fara zaginsa, wasu na barazanar kai masa hari, sai jami’an tsaro suka fitar da shi.

Don kwantar da hankali, Mataimakin Shugaban jam’iyya na kasa, Bukar Dalori, ya mara wa Tinubu da Shettima baya don su ci gaba da mulki.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima dai dan asalin Jihar Borno ne, daya daga cikin jihohin Arewa maso Gabas.

Ganduje ya rikita taron APC kan kalamansa
Taron APC ya koma rigima a Gombe kan goyon bayan Tinubu, Shettima. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Kashim Shettima.
Asali: Twitter

Abin da Ganduje ya ce a taron APC

Taron ya tsaya cak bayan Shugaban jam’iyya na kasa, Abdullahi Ganduje, ya bayyana goyon baya ga Tinubu kadai, ba tare da ambaton Shettima ba.

An ce Ganduje bai ambaci Shettima ko sau daya ba a cikin jawabin sa na kusan mintuna 10 wanda hakan ya fusata mahalarta taron da aka yi Gombe.

Shi ma Ganduje sai da jami’an tsaro suka fitar da shi daga wurin taron domin kare lafiyarsa bayan nuna goyon bayansa ba tare da Shettima ba kamar yadda aka yi zargi.

AIT ta wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna yadda aka yi ta kai ruwa rana a taron da aka gudanar a yau Lahadi.

Inuwa ya goyi bayan Tinubu a zaben 2027

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shugaban kasa Tinubu a zaben 2027.

Inuwa Yahaya ya ce Tinubu ya zuba jari sosai a harkar kiwo, wanda ya haifar da ci gaba, samar da aiki da inganta rayuwar al'umma musamman a Arewacin Najeriya.

Gwamnan ya jinjina wa shugaban kasa bisa amincewa da N120bn domin ci gaban kiwo da kuma noma, yana mai cewa ba a taba haka ba a jihar cikin shekara 47 da suka wuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »