'Gombe Ta Ka Ce': Gwamna Ya ba Tinubu Tabbacin Goyon Bayan Ƴan Jiharsa Gaba Ɗaya
- Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shugaban kasa Tinubu a zaben 2027, yana mai cewa Gombe za ta tsaya masa tsayin daka
- Inuwa Yahaya ya ce Tinubu ya zuba jari sosai a harkar kiwo, wanda ya haifar da ci gaba, samar da aiki da inganta rayuwar al'umma musamman a Arewacin Najeriya
- Gwamnan ya jinjina wa shugaban kasa bisa amincewa da Naira biliyan 120 domin ci gaban kiwo, yana mai cewa ba a taba haka cikin shekara 47 ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bayyana matsayarsa kan goyon bayan shugaban kasa Bola Tinubu.
Inuwa Yahaya ya ce yan Gombe gaba daya suna goyon bayan Tinubu domin sake tsayawa takara a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Asali: Facebook
Gwamna Inuwa ya yabawa Bola Tinubu
Hakan na cikin wata sanarwa da hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Gwamna Inuwa ya bayyana haka a bikin kaddamar da aikin samar da filin kiwo da noma mai fadin hekta 184 a jihar Gombe.
Ya yabawa gwamnatin Tinubu saboda sabbin tsare-tsaren da ta fito da su da suka kawo sauyi da cigaba a fadin kasar nan.
Gwamnan ya ce fannin kiwo ya samu cigaba sosai tun bayan da Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023.
Ƙoƙarin da Tinubu ke yi a Gombe
Gwamna Inuwa ya ce zuba jari da Tinubu ke yi a harkar kiwo yana da burin habaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi da inganta rayuwar jama’a.
Ya bayyana cewa sabon filin kiwo da noma a Gombe ya samu goyon bayan gwamnatin Tinubu, wadda ta amince da N120bn kuma ta fitar da kashi 50 cikin 100.
Ya ce:
“Ina tabbatarwa shugaban kasa cewa saboda abin da ya yi, yake yi, da zai yi, mutanen Gombe za su bi shi har filin yaki ko da ido rufe.
“Zamu yi aiki domin samun nasararsa a 2027, da ikon Allah, sake zabensa tabbas ne."

Asali: UGC
Kaunar da Tinubu ya nunawa al'ummar Gombe
Gwamnan ya ce goyon bayan Tinubu ga fannin kiwo, wanda ke da nasaba da Arewacin Najeriya, yana nuna yadda yake kaunar jama’ar sa.
“Da ba domin shugaban da ke kaunar mutanensa da kuma kwarewa da karfin iko ba, da wannan sauyi bai samu ba.
“Babu wani shugaban Arewa cikin shekaru 47 da ya taba zuba N120bn domin canza fannin kiwo duk da cewa Arewacin Najeriya ke da harkar."
- Cewar Gwamna Inuwa
Gwamna Inuwa ya jinjinawa jajircewar Tinubu na inganta harkar noma da kiwo a Gombe da kuma duk fadin kasar nan.
Ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa duk da kalubale daga gyare-gyaren gwamnati, lokaci mai kyau na gabatowa a karkashin shugabancin Tinubu.
Tattaunawar Legit Hausa da jigon APC a Gombe
Architect Muhammad Abubakar Auwal Akko ya ce babu abin da za su ce sa godiya ga Bola Tinubu saboda abubuwan ci gaba a Gombe.
Ya ce:
"Lallai ba abin da za mu cewa Gwamna Inuwa Yahaya ɗan Majen Gombe na farko sai godiya.
"Domin mu noma da kiwo shi ne gaskiyar mu, gaskiyar kasuwancinmu kenan a Arewa maso Gabas da Arewa gaba daya da kuma Gombe."
Akko wanda hadimi ne ga kakakin majalisar wakilai, Hon. Tajudden Abbas ya ce dukkan wannan nasarori sun samu ne da goyon bayan Tinubu bayan an kai masa korafi ya ba da damar a je a yi, ya kuma ba da rabin kudin.
Ya ce kuma da yardar Allah a 2027 ido rufe za mu yi shi kamar yadda gwamna ya fada, domin ba a taba shugaban da ya kawo mana ci gaba haka ba.
Yan Gombe sun sayawa gwamna ragon layya
A baya, kun ji cewa mazauna unguwar Nayinawa a Gombe sun yi karo-karo, sun sayawa Gwamna Inuwa Yahaya ragon layya don nuna godiya.
Rahotanni sun nuna cewa kyautar ta biyo bayan aikin gyaran babban kwari ne da ke hana shiga unguwar lokacin damina.
Dan Majen Nayinawa ya bayyanawa Legit Hausa cewa aikin ya yaye damuwa ga mutanen da suka dade cikin wahala a unguwar.
Asali: Legit.ng