2027: Wike Ya Yi wa Atiku, El Rufa'i da Masu Hadaka Tabargaza a gaban Tinubu
- Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya ce irin ayyukan da Shugaba Bola Tinubu ke yi sun rusa kawancen ‘yan adawa da ke shirin karɓe mulki a 2027
- Wike ya bayyana haka ne yayin kaddamar da gada da hanyoyi a Abuja, yana mai cewa jam’iyyun adawa ba za su iya tunkarar APC ba saboda rabuwar kawunansu
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na daga cikin fitattun masu jagorantar kokarin kafa kawancen adawa domin fafatawa da Tinubu a zaben 2027
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce ayyukan raya kasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa musamman a Abuja sun jefa kawancen 'yan adawa a matsala.
Nyesom Wike bayyana cewa lamarin zai hana 'yan adawa samun karfi a shirin karbar mulki a 2027.

Asali: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa Wike ya fadi hakan ne a ranar Laraba yayin kaddamar da gadar Maitama-Gishiri da hanyoyin a Katampe, Jahi da Mabushi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Rahoton the Nation ya nuna cewa Wike ya karfafi Tinubu da cewa:
“Kawancen nan ba zai yi nasara ba, kuma ya riga ya mutu. Ayyukanka ne suka kashe shi.”
A cewarsa, jam’iyyun adawa sun kasa kafa tafiya mai karfi saboda babu ci gaba a tsarinsu, kuma suna fama da rikice-rikicen cikin gida.
Halin da Atiku da sauran ‘yan adawa ke ciki
Rahotanni sun nuna cewa wasu fitattun ‘yan adawa sun shiga tattaunawa tun bayan zaben 2023 domin kafa kawancen da zai fafata da Shugaba Tinubu a shekarar 2027.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP, yana daga cikin jagororin wannan yunkuri.
Sai dai har yanzu PDP na fama da rikicin cikin gida wanda ke hana su daidaituwa da tsara shirye-shiryen gaba.

Asali: Facebook
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i da dan takarar shugaban kasa a LP a 2023, Peter Obi suna cikin masu maganar hadaka a Najeriya.
Tinubu ya karfafa 'yan kwangila inji Wike
A yayin jawabin nasa, Wike ya ce gwamnatin Tinubu ta samar da kyakkyawan yanayi da ya dawo da kwarin gwiwar ‘yan kwangila wajen aiwatar da ayyuka a fadin Abuja.
Ministan ya ce:
“A karkashin Tinubu, ‘yan kwangila sun sake samun kwarin gwiwa daga gwamnati. Ayyukanka sun kashe kawancen 'yan adawa a Najeriya.”
A halin yanzu, har yanzu babu wata cikakkiyar jam’iyya ko dandalin da adawa ake amfani da shi domin tunkarar APC, yayin da rikici ke ci gaba da huruwa a cikin PDP, LP da NNPP.
Ana sukar Tinubu kan sauya sunan ICC
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu yana shan kakkausar suka kan sauya sunan dakin taron ICC zuwa sunan shi.
A ranar Talata aka sauya sunan dakin taron da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya gina.
Dr. Hakeem Baba Ahmed da Sanata Shehu Sani na cikin fitattun 'yan Najeriya da suka soki matakin sauya sunan ginin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng