PDP Ta Kara Birkicewa, Manyan Shugabanninta Sun Koma Jam'iyyar APC
- Jam'iyyar PDP mai yin adawa a jihar Legas ta gamu da koma baya bayan wasu jiga-jiganta sun fice
- Mai magana da yawun jam'iyyar tare da wasu manyan shugabanninta sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki a jihar
- Sun bayyana cewa matakin da suka ɗauka ya yi daidai domin jam'iyyar PDP ta riga da ta mutu murus
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Mai magana da yawun PDP na jihar Legas, Hakeem Amode, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar.
Hakeem Amode ya sauya sheƙa daga jam’iyyarsa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Asali: Twitter
Amode tare da wasu fitattun shugabannin PDP sun bayyana sauya sheƙar ne a taron manema labarai da aka gudanar a ranar Litinin a Ikeja, jihar Legas, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ƙusoshin PDP sun sauya sheƙa zuwa APC
The Punch ta ce ya bayyana cewa shi da sauran waɗanda suka sauya sheƙar sun samu ƙwarin gwiwa daga jagorancin hangen nesa na ɗan takarar gwamnan PDP a zaɓen 2023, Abdul-Azeez Adediran (Jandor), wanda shi ma ya riga ya koma APC.
"Yau muna tsaye a gabanku, domin sanar da wani muhimmin mataki da muka ɗauka, mataki wanda ke nuna juyin juya hali ba kawai gare mu kaɗai ba, amma ga ɗimbin masu kishin ci gaban siyasa da suke tare da mu tsawon shekaru."
“A yau, mun yanke shawarar rushe dukkan tsarin jam’iyyar PDP a jihar Legas, daga matakin unguwa har zuwa jiha, domin mu haɗe da mai girma Jandor mu koma gaba ɗaya cikin jam’iyyar APC.”
"PDP a matakin ƙasa da na jiha ta kauce daga ginshiƙan da aka kafa ta a kansu, ginshikan da suka sanya ta zama babbar jam’iyyar siyasa mafi ƙima a nahiyar Afirka."
- Hakeem Amode
Da yake magana a madadin ƴan takarar majalisar dokokin jiha na PDP a zaɓen 2023, Ibrahim Balogun wanda ya tsaya takara a mazabar Kosofe, ya ce ya ɓata shekaru 18 ba tare da wani ci gaba ba a PDP.
“Zamu yi aiki tuƙuru domin ganin nasarar Tinubu a shekarar 2027. Zamu shiga APC gaba ɗaya."
"Jandor jagora ne mai hangen nesa, wanda ya cancanci a bi shi, saboda yana tare da talakawa."
- Ibrahim Balogun

Asali: Original
Shugabannin PDP sun koma APC a Legas
Sauran shugabannin PDP da suka bar jam’iyyar sun haɗa da Prince Rufus Adeniyi, tsohon mataimakin sakataren shirye-shirye na PDP (Legas ta Yamma) da Jerry Afemikhe (Olori Odo), wanda ya tsaya takarar majalisar wakilai a mazaɓar Surulere I.
Hakazalika, Taofeek Obanikoro, Tunde Pratt, Saheed Aregbesola, Sulaimon Thompson, da Taofeek Kuye, duk sun sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Sauran sun haɗa da Adeyemi Kazeem, tsohon shugaban PDP na ƙaramar hukumar Ojo, da Fasto Gbenga Ogunleye, mai taimaka wa ɗan takarar gwamna na PDP a 2023 wajen hulɗa da kafafen yada labarai.
Jigon PDP ya ziyarci Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ƙusa a jam'iyyar PDP, Segun Showunmi, ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Segun Showunmi ya bayyana cewa sun gana da shugaban ƙasan ne bayan ya ziyarce shi a gidansa da ke Legas.
Jigon na PDP ya nuna cewa sun tattauna sosai da shugaban ƙasan kuma tattaunawar ta su ta yi armashi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng