Matasan Arewa Ta Tsakiya Sun Watsa wa Shugaba Tinubu Ƙasa a Ido Tun kafin Zaɓen 2027

Matasan Arewa Ta Tsakiya Sun Watsa wa Shugaba Tinubu Ƙasa a Ido Tun kafin Zaɓen 2027

  • Matasan Arewa ta Tsakiya sun bayyana Dr. Gbenga Olawepo-Hashim a matsayin wanda suke goyon bayan ya karbi shugabancin Najeriya a 2027
  • A cewar matasan, lokaci ya yi da yankin zai tashi tsaye ya nemi shugabancin Najeriya tare da kawo ƙarshen wariyar da ake nuna masa
  • Matasan sun ce Gbenga Olawepo-Hashim mutum ne mai gogewa, wanda zai iya maganin duka matsalolin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gamayyar kungiyoyin matasa daga yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya ta bayyana goyon bayanta ga Dr. Gbenga Olawepo-Hashim a matsayin zabinsu na takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Matasan sun kuma yi kira da a kawo karshen shekaru masu tsayi da aka diba ana nuna wariyar siyasa da buƙatar tabbatar da adalci da daidaito a tsarin mulkin kasar nan.

Dr. Gbenga Olawepo-Hashim.
Matasan Arewa ta Tsakiya sun haɗa kai, sun goyi bayan Dr. Gbenga Olawepo-Hashim Hoto: Gbenga Olawepo-Hashim
Asali: Facebook

Sun bayyana wannan goyon baya ne a taron manema labarai da suka gudanar a Abuja, karkashin jagorancin kungiyar Youth for the Actualization of North Central President (YANCP), Tribune Nigeria ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Shugaba Tinubu ya gamu da cikas a Arewa

Da yake jawabi a wurin taron, shugaban YANCP na kasa, Kwamared Ibrahim Musa, ya bayyana goyon bayan kungiyar ga Dr. Olawepo-Hashim domin ya karɓe shugabancin Najeriya a 2027.

Ya ce yankin Arewa ta Tsakiya ya dade yana ba da gudummiwa a Najeriya amma ana ci gaba da wulakanta shi wajen shugabancin kasa.

Ibrahim Musa ya ce:

“Yankinmu na Arewa ta Tsakiya ya sha wahala, ya ba da gudummuwa gagara misali a lokuta da dama a tarihin Najeriya, amma har yanzu mune a gefe idan aka zo batun manyan mukaman shugabanci.
"Wannan zalunci ya kamata ya zo ƙarshe, kuma muna hangen alheri a jikin Olawepo-Hashim, muna da yaƙinin zai zama jagora na gari."

Wa matasan Arewa ta Tsakiya suke goyon baya?

Dr. Olawepo-Hashim, ya taba tsaya wa takarar shugaban kasa a baya kuma fitaccen dan gwagwarmaya ne a tsarin dimokuradiyya.

Ya taɓa rike mukamin mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP ta ƙasa a baya, kuma ya shahara a matsayin dan gwagwarmaya mara tsoro.

Shugabannin YANCP sun ce gogewarsa a fannin kasuwanci da sanin makamar aiki ya sa suke ganin shi ya dace ya tukari matsalolin Najeriya.

Gbenga Olawepo-Hashim ya samu goyon baya.
Matasan Arewa Ta Tsakiya sun ce lokaci ya yi da za a ba su dama su shugabanci Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Gbenga Olawepo-Hashim
Asali: Facebook

A rahoton Guardian, sakatariyar YANCP ta ƙasa, Fatima Tanko ta ce:

“Mun gaji da wannan siyasa ta wasu yankuna ƙalilan ‘yan siyasa guda. Dr. Hashim yana da zurfin ilimi, hangen nesa a fannin tattalin arziki, da halaye nagari.
"Ba wai kawai ɗan yankin Arewa ta Tsakiya ba ne, shi dan Najeriya ne gaba daya.”

Matasan Arewa sun soki Shugaba Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar matasan Arewacin Najeriya ta nuna damuwa kan yadda Shugaba Tinubu ya ƙi miƙa mulki ga Kashim Shettima lokacin da ya yi tafiya.

Matasan sun bayyana cewa hakan ya saba da kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma yana ƙara nuna yadda ake neman watsi da Arewa a gwamnatin Tinubu.

Sun ce kundin tsarin mulki ya fayyace yadda za a mika mulki idan shugaban kasa ba ya nan ko kuma ba ya iya sauke.nauyin ofishinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »