'Ban da Matsala da Kai': Matawalle Ya Shawarci Dauda Lawal kan Zuwa APC
- Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya tura sako na musamman ga Gwamna Dauda Lawal kan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
- Matawalle ya buƙaci Gwamna Lawal da ya bar PDP zuwa APC, yana cewa jam’iyyar na da nagarta da mutane masu hangen nesa
- Ministan ya fadi hakan ne a Maradun yayin da dubban magoya bayansa suka kai masa gaisuwar Sallah, yana mai kira kan hadin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maradun, Zamfara - Karamin Ministan Tsaro a Najeriya, Dr.vBello Matawalle, ya yi magana kan gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na Zamfara.
Matawalle ya gayyaci gwamnan Zamfara, Dauda Lawal da ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar.

Asali: Twitter
Matawalle ya yi wannan kiran ne a Maradun yayin da dubban magoya bayansa suka kai masa gaisuwar Sallah, cewar BBC Hausa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Dauda Lawal ya musanta shirin zuwa APC
Wannan kira na Matawalle na zuwa ne bayan Gwamna Dauda Lawal ya fayyace gaskiya game da jita-jitar cewa zai koma jam'iyyar APC.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Dauda Lawal ya ƙaryata zarge-zargen da ake yi masa kan komawa APC mai mulkin Najeriya.
Gwamnan ya tabbatar da cewa shi cikakken dan jam'iyyar PDP ne kuma mai kishinta har cikin ransa inda ya bukaci al'umma su yi watsi da labarin da ake yaɗawa.
An yi yaɗa jita-jitar lokacin da ake rade-radin wasu gwamnoni suna ganawa da manyan APC domin shirin komawa APC a kasar.
Yadda Dauda Lawal ya lashe zaben Zamfara
Matawalle shi ne tsohon gwamnan Zamfara wanda Gwamnan Dauda Lawal ya yi nasarar kwace mulki a hannunsa a zaben 2023.
Tsohon gwamnan wanda yanzu shi ne karamin ministan tsaro ya sha kaye ne bayan yin wa'adi daya kacal a kan mulkin jihar daga 2019 zuwa 2023.

Asali: Facebook
Matawalle ya fadi mutanen da ke shiga APC
Matawalle ya ce APC jam’iyya ce da ke cike da mutane na gari, yana mai ƙarfafawa DaudacLawal guiwa da ya shiga jam’iyyar domin ciyar da jiharsa gaba.
A cewarsa:
"Ba ni da matsala da gwamna Dauda Lawal idan yana son shiga jam'iyyarmu ta APC.
"Ya zo ya bi sahun masu yunkurin kawo kawo ci gaba a kasa da hangen nesa."
Ya kuma bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu mutum ne mai hangen nesa da ke son zaman lafiya, kuma ya mayar da hankali kan ci gaban ƙasa.
Matawalle ya gwangwaje yan Zamfara da kyauta
Mun ba ku labarin cewa yayin da ake bukukuwan babbar sallah, karamin ministan tsaro, Alhaji Bello Matawalle, ya yi rabon raguna ga mambobin APC.
Matawalle ya ba da gudunmawar raguna 3,000 ga magoya bayan jam’iyyar APC a jihar Zamfara domin sauƙaƙa musu bukukuwan Sallah duba da halin da ake ciki a kasa.
Kyautar ragunan da ministan ya yi, za a raba ta ne a dukkanin ƙananan hukumomi 14 da ke faɗin jihar domin yin bukukuwan sallah cikin walwala.
Asali: Legit.ng