'Goron Sallar Tinubu ce': A ƙarshe, Gwamna Ya Jero Dalilansa na Komawa Jam'iyyar APC

'Goron Sallar Tinubu ce': A ƙarshe, Gwamna Ya Jero Dalilansa na Komawa Jam'iyyar APC

  • Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom ya fadi dalilansa na komawa jam'iyyar APC inda ya yabawa Bola Tinubu tun lokacin da yake Gwamnan Lagos
  • Eno ya ce cire tallafin fetur ya sa gwamnoni suka fi samun kudi, inda ya bayyana alherin da Akwa Ibom ke samu
  • Ya ce wannan sauyin siyasa hadaya ce ga Tinubu a ranar Sallah, yana kuma tabbatar da goyon bayansa ga ayyukansa na musamman

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana dalilinsa na komawa jam'iyyar APC.

Eno ya ce ya shiga jam’iyyar APC ne saboda tarihin nasarorin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna ya jero dalilansa na shiga APC
Gwamna Eno ya yabawa salon mulkin Tinubu. Hoto: Pastor Umo Eno.
Asali: Twitter

Gwamna ya magantu bayan komawa APC

A cewarsa, tun lokacin da Tinubu ke Gwamnan Lagos, ya fara sha’awarsa saboda yadda ya sauya jihar, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Ya kara da cewa a matsayinsa na Shugaban kasa, Tinubu ya nuna jarumta wajen tinkarar matsalolin tattalin arzikin kasa tare da daukar matakai masu wuya.

A cewarsa:

"Shugaba Tinubu, wat kila shi ne ya fuskanci matsalolin tattalin arziki mafi wahala cikin 'yan kwanakin nan na tarihin kasar nan.
“Da jarumta da gaskiya, ya fuskanci wadannan kalubalen kai tsaye ya kuma kawo mafita da ke da tasiri mai dorewa duk da wuya a farko.
“Cire tallafin fetur, duk da kuwa ya kasance mataki mai tsanani, ya bai wa jihohi karin kudi don aiwatar da ayyukan raya jama’a.

Ya kara da cewa:

“Na dade ina nuna sha’awa ga Shugaban kasa da kishin kasarsa da kokarinsa wajen farfado da kasa da al’umma gaba daya."
Gwamna ya yabawa salon mulkin Tinubu
Gwamna Umo Eno ya fadi dalilin shiga APC. Hoto: Pastor Umo Eno, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Alkawarin da gwamna Eno ya yiwa Tinubu

Gwamna Eno ya ce sauyinsa zuwa APC kyauta ce ga Tinubu, yana mai cewa yana da cikakken yakini da gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Shugaba Tinubu.

“Ga wadanda ke nuna damuwa da wannan sauyin, zan tabbatar da cewa na samu cikakken goyon baya daga Shugaba Tinubu da Sanata Godswill Akpabio.”
“Wadanda suka san Shugaban kasa, sun san cewa kalamansa gaskiya ne. Wannan sauyi da ya zo a Sallah, hadaya ce gare shi."

- Cewar gwamna Eno

Eno ya yi alkawarin tafiyar da gwamnati mai hada kowa da kowa bisa ajandar 'Renewed Hope' da 'ARISE' na gwamnatin tarayya da ta jihar, Vanguard ta ruwaito.

Ya kara da cewa:

“Don me na shiga APC? Amsa tana da sauki: Don moriyar jiharmu, da bukatar daidaita da Gwamnatin Tarayya don samun karin cigaba.
“Mu hade gaba daya, mu taso da karfi, mu gina Akwa Ibom, ya fi hada kai, da cigaba bisa ajandar 'Renewed Hope."

Bayan komawar gwamna APC, Kwamishina ya yi murabus

Kun ji cewa Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya rasa kwamishinansa ƙasa da awa ɗaya bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Kwamishinan ayyuka na musamman, Mista Ini Ememobong ya yi murabus daga muƙaminsa saboda ba zai iya bin gwamnan ba.

Ya ce duk da ya bar gwamnatin Fasto Umo Eno, zai ci gaba da girmama shi a matsayinsa na ɗan uwa, wanda ya aminta da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »