Gwamnan Osun Ya Gana da Tinubu kan Shirin Sauya Sheƙa zuwa APC? An Samu Bayanai
- Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun tare da ƴan uwansa sun ziyarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke Legas
- Wannan ziyara ta sake dawo da raɗe-raɗin cewa Gwamna Adeleke na shirin sauya sheƙa zuwa APC gabanin zaɓen Osun 2026
- Kakakin gwamna, Olawale Rasheed ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa, yana mai cewa Gwamna Adeleke na nan daram a jam'iyyar PDP
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun - Mai magana da yawun Gwamna Ademola Adeleke, Olawale Rasheed, ya ce ziyarar da dangin Adeleke suka kai wa Shugaba Bola Tinubu ba ta da nasaba da batun sauya sheka.
A ranar Talata, Gwamna Adeleke tare da ɗan uwansa, Dr. Deji Adeleke, da ɗansu, mawaki David Adeleke (Davido), suka kai ziyara ga Shugaba Tinubu a Legas.

Asali: Facebook
Gwamna Adeleke ya wallafa hotunan ziyarar da suka kai wa shugaban ƙasa a shafinsa na X ranar Talata, 3 ga watan Yuni, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Wannan ziyara ce mutane suka fassara ta da cewa gwamnan Osun na shirin ficewa daga PDP ya koma APC.
Da gaske gwamnan Osun zai koma APC?
Sai dai a cikin wata sanarwa da Mista Olawale ya fitar a ranar Laraba a shafin X, ya bayyana cewa wannan ziyara ba wani abu ba ne face gaisuwar ban girma ga shugaban ƙasa.
Kakakin gwamnan Osun, ya ce:
“Zancen da ake yadawa a kafafen yaɗa labarai cewa gwamna Adeleke na shirin sauya sheka ƙarya ce.
"Har yau, Gwamna Adeleke mamba ne kuma jagora na jam’iyyar PDP a Jihar Osun.
“Ziyarar da iyalan gidan Adeleke suka kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu gaisuwar ban girma ce kawai. Duk wata fassarar cewa suna shirin sauya sheka ƙarya ce.”
APC ta musanta batun sauya shekar Adeleke
A nata ɓangaren, APC ta Jihar Osun, ta bakin tsohon Kakakin Majalisar Dokoki, Timothy Owoeye, ta ce tikitin takarar gwamna na jam’iyyar a 2026 ba na siyarwa ba ne.
Mista Owoeye ya kuma bayyana cewa ba su buƙatar Gwamna Adeleke ya dawo cikin jam'iyyar APC a yanzu.

Asali: Twitter
A cewarsa:
“Ina faɗin hakan a fili don kowa ya san cewa tikitin APC ba na siyarwa ba ne. A zahirin gaskiya, har zuwa yau, ba mu ɗauki Gwamna Adeleke a matsayin mamba ko wani ɓangare na APC ba.
“APC ita ce jam'iyya mai nasara, ba don fargabar da iyalan Adeleke ke yi na rasa mulki ba, ba za su nuna sha'awar shigowa APC ba.
“A ranar 8 ga watan Agusta, 2026, zamu kori PDP daga gadon mulkin jihar Osun. Muna roƙon al’umma su zauna lafiya, babu wurin PDP ko Adeleke a jam’iyyar APC.”
Ƴan Majalisar Osun sun yi saɓani kan Adeleke
A wani labarin, kun ji cewa sabani ya shiga tsakanin 'yan majalisar Osun, Bamidele Salam da Oluwole Oke, kan zargin zawarcin Gwamna Ademola Adeleke zuwa APC.
Jiga-jigan biyu sun fara samun saɓani ne bayan da aka fara yaɗa labarin cewa shugabannin APC sun fara kokarin shawo kan gwamna ya dawo jam'iyyar.
Hon. Salam, ya yi zargin cewa jagorori APC sun fara zawarcin Adeleke yayin da Hon Oke ya soki wannan zargi da takwaransa ya yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng