Ondo: Kotu Ta Raba Gardama kan Shari'ar da Ke Neman Tsige Gwamnan APC
- Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Ondo ta tabbatar da nasarar Lucky Aiyedatiwa, ta kuma yi watsi da ƙarar jam'iyyun PDP da SDP
- Alkalin kotun, Benson Ogubu, ya ce PDP da dan takararta Agboola Ajayi sun kasa tabbatar da zargin magudi a zaben 2024 da aka gudanar a jihar
- Aiyedatiwa na APC ya samu kuri’u 366,781 a kan abokan takararsa a kananan hukumomi 18 wanda hukumar INEC ta bayyana shi a matsayin zakara
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Akure, Ondo - Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Ondo da ke zamanta a Akure ta raba gardama kan takaddama da ake yi.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa, ta kuma yi watsi da kararraki da dama da ke kalubalantar nasararsa a zaben da aka yi a 2024.

Asali: Twitter
Kotu ta yi hukunci kan shari'ar zaben Ondo
Rahoton Channels TV ya tabbatar da cewa an gudanar da zaben ne a ranar 16 ga Nuwamba, 2024 wanda Aiyedatiwa na APC ya samu nasara mai rinjaye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
A hukuncin da aka yanke ranar Laraba wanda ya dauki fiye da awa takwas, kotun mai Alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari'a, Benson Ogubu ta tabbatar da hukuncin.
Kotun ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta Agboola Ajayi suka shigar saboda zargin tafka magudi da rashin bin ka'ida.
Dan takarar PDP ya bayyana cewa “akwai yaduwar rashin daidaito” a zabukan, inda ya nemi kotun ta soke sakamakon zaben da aka fitar.
Kotun ta kuma yi watsi da sauran kararraki iri daya daga wasu jam’iyyu kamar SDP, ADC, APM da AA, wadanda dukkansu suka kalubalanci sahihancin zaben.

Asali: Facebook
Yadda Aiyedatiwa ya yi nasara a zabe
Hukumar INEC ta bayyana Gwamna Aiyedatiwa, wanda ya tsaya takara karkashin jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben a kananan hukumomi 18 na jihar.
Ya samu jimillar kuri’u 366,781 inda ya kayar da abokan takararsa ciki har da Ajayi na jam’iyyar PDP, wanda ya zo na biyu a sakamakon zaben, cewar Punch.
Da wannan hukunci, kotun ta tabbatar da sahihancin nasarar Aiyedatiwa a matsayin gwamna wanda ya gaji kujerar bayan mutuwar mai gidansa, Rotimi Akeredolu.
Hakan ya kawo karshen shari’ar da ke tattare da zaben gwamna na 2024 duk da sauran bangarori ka iya daukaka kara zuwa kotunan gaba domin neman adalci kan lamarin.
Gwamna Aiyedatiwa ya yi nasara kan NNPP
Kun ji cewa jam'iyyar NNPP da ɗan takararta na gwamna a Ondo, Hon. Gbenga Edema sun yi rashin nasara a karar da suka kalubalanci Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar.
Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Akure ta kori karar da NNPP da Edema suka nemi tsige mai girma Lucky Aiyedatiwa da mataimakinsa a zaɓen da aka yi a shekarar 2024.
A cewar masu ƙara, an tafka wasu kura-kurai a zaben fitar da gwanin da APC ta yi wanda Gwamna Aiyedatiwa ya samu nasara cikin sauran wadanda suka fafata tare da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng