Sanata Barau Ya Sake Raunata Tafiyar Kwankwasiyya a Kano

Sanata Barau Ya Sake Raunata Tafiyar Kwankwasiyya a Kano

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Barau Jibrin, ya tarbi wasu mambobin Kwankwasiyya da suka tsallaka zuwa jam'iyyar APC
  • Sanata Barau Jibrin ya yaba musu kan matakin da suka ɗauka, ya bayyana cewa sun rabu da tafiyar da take talauta mutane da sanya su cikin damuwa
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan, ya buƙaci masu sauya sheƙar da su marawa shugaban ƙasa Bola Ahmeɗ Tinubu baya don ya samu nasara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya karɓi ɗaruruwan mambobin Kwankwasiyya da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Sanata Barau Jibrin mai wakitar Kano ta Arewa ya bayyana sauya sheƙarsu a matsayin wani nufin ubangiji na samar musu da kyakkyawar makoma ta siyasa.

Sanata Barau Jibrin
Sanata Barau ya tarbi 'yan kwankwasiyya a Kano Hoto: @baraujibrin
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne yayin taron karɓar su da aka gudanar a Kano, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Barau Jibrin ya tarbi ƴan Kwankwasiyya

Sanata Barau ya yabawa sababbin mambobin, yana mai cewa shawarar da suka yanke ta shiga APC ta zo a kan lokaci kuma tana da matuƙar amfani.

“Duk lokacin da Allah Ya nufi Ya kyautata rayuwarka, sai ya shiryar da kai zuwa hanya madaidaiciya. Na yi imani cewa Allah ne ya kawo ku cikin APC domin inganta rayuwarku."

- Sanata Barau Jibrin

Sanata Barau ya bambanta APC da tafiyar Kwankwasiyya, inda ya zargi tafiyar da haifar da ruɗani da talauci.

"Yayin da APC ke ginawa, jam’iyyar da kuka bari ita ce ke rushewa."

- Sanata Barau Jibrin

Sanata Barau ya soki tafiyar Kwankwasiyya

Ya ƙara da cewa mutane da dama sun yi asarar rayuka, dukiya da ma lafiyar kwakwalwa saboda shiga tafiyar Kwankwasiyya.

Yayin da ya ke kwatanta tafiyar da sunan “kwan-kwa-tsiya,” wato “haifar da talauci,” Sanata Barau ya buƙaci sababbin mambobin da su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya kuma buƙaci su ba da gudunmawa wajen ƙarfafa nasarorin APC a Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Taron karɓar masu sauya sheƙar ya samu halartar manyan jiga-jigan APC, shugabanni da kuma waɗanda suka sauya sheƙar, inda suka sha alwashin biyayya ga jam’iyyar mai mulki.

Sanata Barau Jibrin
Sanata Barau ya amshi 'yan Kwankwasiyya zuwa APC Hoto: @baraujibrin
Asali: Twitter

Karanta wasu labaran kan Sanata Barau

Kano: Gangar siyasar 2027 ta fara zaƙi, an nemi Barau ya yi takarar gwamna da Abba

Kawu Sumaila ya hada kai da Barau wajen yi wa NNPP da Abba barna a Kano

Rikicin Kwankwasiyya ya budewa Barau kofar karbar 'yan NNPP zuwa APC a Kano

Siyasar Kano: Kwankwaso da 'yan APC

Sanata Barau Jibrin da 'yan tsagin Kwankwaso na ci gaba da samun sabani a siyasar Kano, lamarin da ke haifar da juyin juya hali cikin jam’iyyu da kuma sauyin mabiya daga wannan gida zuwa wancan.

Duk da kasancewarsu ‘yan asalin jihar Kano, Barau da Kwankwaso na fuskantar bambancin akida da dabaru a tafiyar da siyasa, musamman wajen nuna wa talakawa alkibla mai amfani.

Sanata Barau, wanda ke matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa, ya dade yana jaddada cewa tafiyar Kwankwasiyya ba ta amfanar talaka sai dai ta jefa shi cikin rudani da matsin rayuwa.

Wannan ya sa yake karɓar masu sauya sheƙa daga Kwankwasiyya zuwa APC tare da bayyana su a matsayin waɗanda Allah ya shiryar da su zuwa hanya madaidaiciya.

Siyasar Kano dai ta shahara da samun sauyin lamura cikin gaggawa, inda mutum zai wayi gari yana da dimbin mabiya amma ya farka gobe ya rasa su.

A yau, Kwankwaso na da masoya a fannoni da dama, amma Barau na ƙara samun goyon baya musamman daga yankin Kano ta Arewa.

Wannan takaddama na nuna cewa siyasar Kano ba ta da tabbas — mai iko yau na iya zama maras tasiri gobe.

Ƙungiyar Kwankwasiyya ta ja kunnen Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungigar Kwankwasiyya ta aika da saƙon gargaɗi ga Gwamna Abba Kabir na jihar Kano.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnan na Kano da ya yi taka tsan-tsan da wasu mutane da ke cikin majalisar zartarwarsa.

Ƙungiyar ta nuna cewa akwai wasu mutane da ke cikin majalisar zartarwar, waɗanda suke ƙoƙarin cimma wasu manufofi daban da na Gwamna Abba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta [email protected]

OSZAR »