'Wike Ya Fara Nuna Alamun Zagin Tinubu,' Abati Ya Gargadi Shugaban Kasa

'Wike Ya Fara Nuna Alamun Zagin Tinubu,' Abati Ya Gargadi Shugaban Kasa

  • Reuben Abati ya ce Nyesom Wike mutum ne mai rashin kunya da rashin girmama manyan da suka taimake shi a siyasa
  • Ya zargi Wike da zagin tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, wanda ya ce shi ne uban gidansa a siyasa a baya
  • Abati ya yi gargadin cewa Ministan zai iya juya baya, ya zagi Bola Tinubu, kamar yadda ya rika zagin wasu da suka taimake shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon mai magana da yawun Goodluck Jonathan, Reuben Abati, ya bayyana Ministan Abuja, Nyesom Wike, a matsayin ɗan siyasa marar ladabi da kuma girman kai.

A cewar Abati, Wike ya saba raina waɗanda suka ba shi dama a siyasa, ciki har da Rotimi Amaechi da Peter Odili, waɗanda suka taka rawa wajen ganin ya kai matsayin da yake kai.

Tinubu
Abati ya ce Wike zai iya zagin Tinubu a gaba. Hoto: Nyesom Ezonwo Wike|Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa Abati ya ce ba mamaki watarana Wike ya zagi Tinubu kamar yadda ya yi wa wasu iyayen gidansa a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Jawabin Dr. Abati ya zo ne bayan wata hira da Wike ya yi a kafar yada labarai, inda ya soki Amaechi da cewa "ba yunwar abinci suke ji ba, yunwar mulki ce ke damunsu."

An zargi Nyesom Wike da rashin ladabi

Business Day ta wallafa cewa Abati ya ce Wike ya nuna rashin girmamawa ga Amaechi, wanda ya ce ya ba shi dama tun lokacin da yake shugabantar ƙaramar hukuma.

Abati ya kara da cewa Wike ya fara zagin Amaechi ne bayan ya samu dama da matsayi, duk da cewa shi ne ya tsaya masa har ya zama shugaban ƙaramar hukuma da kuma Minista daga baya.

Ya ce wannan dabi’a ce ta rashin godiya da nuna cewa Wike baya ganin kowa sai kansa, yana mai gargadin cewa irin wannan hali na iya shafar Shugaba Tinubu nan gaba.

Reuben Abati: 'Wike ya saba zagin manya'

Abati ya yi nuni da cewa kafin yanzu Wike ya zagi Peter Odili, wanda shi ma tsohon gwamna ne a Jihar Ribas kuma ya taimaka masa wajen hawa kujerar gwamna a 2015.

Haka kuma ya ambaci cewa Wike ya taba zagin Sanata John Mbata, wanda ya ce ya zama jagora a siyasar Wike a lokacin da ya fara tasowa.

Abati ya ce wannan tarihi na nuna cewa Wike bai taɓa ƙyale wanda ya taimake shi ba, kuma hakan ya sa ake fargabar cewa Shugaba Tinubu ba zai zama na daban ba.

Abati ya gargaɗi Tinubu kan Wike

Reuben Abati ya gargadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ji tsoron hulɗa da Wike, yana mai cewa alamun da Wike ke nunawa na iya kai ga cin mutuncinsa a nan gaba.

Ya ce a hirar da Wike ya yi kwanan nan, ya furta cewa da ya san cewa Shugaba Tinubu zai ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas, da bai ba shi shawarar da ya ba shi ba tun farko.

Abati
Abati ya gargadi Tinubu kan hulda da Wike. Hoto. Rueben Abati|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Abati ya ce wannan magana na nuni da cewa Wike yana gina hujja da za ta ba shi damar zagin Shugaban kasa, idan ya ga dama a siyasa ko ya samu sabani da shi a nan gaba.

An kai karar Wike wajen Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa wani lauya mai kare hakkin dan Adam ya bukaci Bola Tinubu ya taka birki wa Nyesom Wike.

Lauyan ya bayyana cewa Wike na kashe kudin gwamnati ba bisa ka'ida ba wajen yin taron manema labarai duk wata.

A karkashin haka lauyan ya bukaci Tinubu ya hana shi yin hirar domin amfani da kudin ta wasu hanyoyin da suka dace.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »