Shugabanni 2 a Majalisa Sun Yi Murabus, An Naɗa Sababbi don Ɗinke Ɓarakar da Ta Kunno a APC
- Majalisar Dokokin Jihar Ondo ta yi wasu ƴan sauye-sauye tsakanin shugabanninta a yau watau Talata, 3 ga watan Yuni, 2025
- Mataimakin Kakakin majalisa, Abayomi Akinruntan, da shugaban masu rinjaye, Emmanuel Ogunmolasuyi sun miƙa takardar ajiye muƙamansu
- Shugabannin biyu sun yi murbaus ne domin mutunta yarjejeniyar raba muƙamai, ƴan Majalisa sun zaɓi mambobi biyu da za su maye gurbinsa nan take
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ondo, Hon. Abayomi Akinruntan, ya yi murabus daga mukaminsa yau Talata, 3 ga watan Yuni, 2025.
Haka nan kuma shugaban masu rinjaye na Majalisar dokokin Ondo, Hon. Emmanuel Ogunmolasuyi, ya bu sahunsa, shi ma ya ajiye muƙamisa.

Asali: Facebook
Me yasa shugabannin majalisa suka yi murabus?
Jaridar Punch ta tattaro cewa shugabannin biyu sun ajiye muƙamansu a Majalisa saboda mutunta yarjejeniyar raba muƙamai a tsakanin yankunan jihar Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Hon. Akinruntan shi ne mamba mai wakiltar Mazabar Ilaje ta 1, yayin da Ogunmolasuyi ke wakiltar Mazabar Owo ta 1 a Majalisar dokokin jihar da ke Kudu maso Yamma.
Duka ƴan Majalisun biyu mambobin jam'iyyar APC ne mai mulki a jihar Ondo da ma Najeriya baki ɗaya.
Yadda ƴan majalisar 2 suka ajiye muƙamansu
Shugabannin guda biyu sun sanar da murabus dinsu ne a wasiƙin da suka miƙa a zaman majalisar dokokin, wanda ya gudana a ranar Talata.
Kakakin Majalisar Dokokin Ondo, Rt. Hon. Olamide Oladiji, ne ya jagoranci zaman a zauren Majalisar da ke birnin Akure.
Hon. Akinruntan ya bayyana cewa yarjejeniyar rabon madafun iko a siyasar jihar ce ta sanya shi yin murabus daga mukaminsa, rahoton Daily Trust.
“Ina miƙa takardar murabus ɗina daga mukamin Mataimakin Kakakin Majalisar, wanda zai fara aiki daga yau, 2 ga Yuni, 2025.
“Na yanke shawarar yin murabus ne don mutunta tsarin rabon madafun iko da aka saba bi wajen raba mukamai a jihar.
"Ina matuƙar godiya ga dukkan ‘yan majalisa da ma’aikata bisa gudunmawarsu da goyon bayansu,” in ji shi.

Asali: Facebook
Majalisa ta zaɓi waɗanda za su maye gurbinsu
Rahotanni sun nuna cewa bayan murabus dinsu, ƴan Majalisar sun zaɓi waɗanda za su maye kujerunsu nan take.
Waɗanda aka zana domin maye gurbinsu sun haɗa da Hon. Ololade Gbegudu mai wakitar Mazabar Okitipupa ta 2 a matsayin sabon Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Ondo.
Sai kuma Hon. Olatunji Oshati, wanda ke wakiltar mazabar Ose, da aka zaɓa a matsayin sabon Shugaban Masu Rinjaye a Majalisa.
Ana ganin wannan sauyi da aka samu a Majalisar zai kawo karshen rikicin siyasar da ake raɗe-raɗin zai kunno kai a jam'iyyar APC mai mulki a Ondo.
Gwamna ya shiga aji ya koyar da ɗalibai
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Ondo, Hon. Lucky Aiyedatiwa ya ba jama'a da dama mamaki yayin da aka gan shi a aji yana koyar da ɗalibai a a wata makaranta.
A cikin wani faifan bidiyon da aka wallafa, an ga Gwamna Aiyedatiwa ya rubuta kalmar "Drugs" watau magunguna a kan allo yana kuma tambayar ɗalibai su faɗi nau’ikan magunguna.
Wannan lamari na zuwa ne makonni bayan gwamnan ya amince da daukar sababbin malamai 1,100 domin koyarwa a makarantun gwamnati da ke faɗin jihar.
Asali: Legit.ng