Ministocin Buhari da Suka Bari ko Ake Tunanin Za Su Iya Watsi da Jam'iyyar APC
FCT, Abuja - Yayin da aka fara kaɗa kugen siyasar 2027, akwai wasu daga cikin ministocin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da suka fice daga APC.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Wasu daga cikin waɗannan ministocin dai sun taka rawa wajen kafa jam'iyyar APC kafin shigarta babban zaɓen shekarar 2015.

Asali: Facebook
Ministocin Buhari da suka bar APC
Daga cikin ministocin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, akwai guda uku da suka sanar da ficewarsu daga jam'iyyar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Kowane daga cikinsu ya bayyana mabambantan ra'ayoyi kan dallilansu na yin bankwana da jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Ga jerinsu a nan ƙasa:
1. Solomon Dalung

Asali: Getty Images
Solomon Dalung wanda ya riƙe muƙamin ministan wasanni a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya fice daga APC a watan Afrilun 2022, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Solomon Dalung ya bayyana cewa abubuwan da suke faruwa a jam'iyyar sun saɓa kan yadda yake kallon ya kamata a riƙa gudanar da harkokin jam'iyyar.
Bayan ficewarsa daga APC, Solomon Dalung ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar SDP.
2. Rauf Aregbesola

Asali: Twitter
Rauf Aregbesola wanda ya riƙe muƙamin ministan harkokin cikin gida a gwamnatin Muhammadu Buhari, ya fice daga jam'iyyar APC a watan Janairun 2025.
Tsohon gwamnan na jihar Osun ya fice daga APC ne tare da ƙungiyarsa ta 'Omoluabi Progressives', cewar rahoton jaridar TheCable.
Har ya zuwa yanzu Aregbesola bai koma wata jam'iyya ba, amma ana hasashen zai shiga cikin haɗakar jam'iyyun ƴan adawa wacce Atiku Abubakar ke jagoranta.
3. Mohammed Abdullahi

Asali: Twitter
Tsohon ministan wasanni, Mohammed Abdullahi, ya fice daga jam'iyyar APC a ranar, 2 ga watan Yunin 2025.
Mohammed Abdullahi wanda ya riƙe muƙamin ministan muhalli a gwamnatin Shugaba Buhari, ya ce ya bar APC ne saboda wasu dalilai na shi na ƙashin kansa,cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Tsohon ministan bai bayyana inda akalar siyasarsa za ta dosa ba, bayan sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC.
Ministocin Buhari da za su iya barin APC
Duk da dai har yanzu suna cikin APC, akwai wasu daga cikin ministocin Muhammadu Buhari da ake hasashen cewa za su iya barin jam'iyyar.
Wasu saga cikinsu sun fito fili sun caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yayin da aka hango wasu kuma suna ɗasawa da tafiyar haɗakar jam'iyyun ƴan adawa.
Ga jerinsu a ƙasa:
1. Rotimi Amaechi

Asali: Facebook
Tsohon ministan sufuri a gwamnatin Buhari, Rotimi Amaechi na daga cikin mutanen da ake yi wa kallon za su fice daga jam'iyyar APC.
Amaechi wanda ya taɓa yin gwamnan jihar Rivers, ya shiga cikin haɗakar jam'iyyun ƴan adawa, amma har yanzu bai sanar da ficewarsa daga APC ba.
A baya-bayan nan ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda ya bayyana cewa duk an maida ƴan Najeriya mayunwata.
2. Abubakar Malami

Asali: Facebook
Akwai alamun Abubakar Malami wanda ya riƙe muƙamin ministan shari'a a gwamnatin Buhari, ya fice daga jam'iyyar APC.
Abubakar Malami wanda yake cikin tsohuwar jam'iyyar CPC ta Buhari kafin ta haɗe cikin APC, ya nuna rashin gamsuwarsa da wasu abubuwan da ke faruwa a jam'iyyar.
Tsohon ministan ya fito ya caccaki APC, yana mai cewa maimakon ta maida hankali wajen magance matsalolin da ƴan Najeriya suke ciki, ta koma tana nuna goyon baya ga tazarcen Bola Tinubu a 2027.
Malami wanda har yanzu bai fice daga APC ba, ana hasashen cewa zai shiga cikin tafiyar haɗakar jam'iyyun ƴan adawa.
3. Emeka Nwajiuba
Tsohon ministan ilmi a gwamnatin Buhari, Emeka Nwajiuba na daga cikin mutanen da ake hasashen za su bar jam'iyyar APC.
Emeka Nwajiuba ya yi takara da Shugaba Tinubu a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na APC a shekarar 2022.
Ana ganin cewa akwai yiwuwar tsohon ministan ya shiga cikin haɗakar jam'iyyun ƴan adawa don neman kifar da Tinubu a zaɓen 2027.
Buhari ya taya Tinubu murna
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya taya Shugaba Bola Tinubu murna.
Muhammadu Buhari ya taya shugaban ƙasan murna ne kan cikarsa shekara biyu a kan madafun ikon Najeriya.
Tsohon shugaban ƙasan ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da gwamnatin Tinubu kan manufofin da ta ɓullo da su, inda ya ce gyara bai faruwa kwatsam a lokaci ɗaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng