Rigima Ta Barke tsakanin 'Yan Majalisar Wakilai, Ana Zargin APC Na Zawarcin Gwamna

Rigima Ta Barke tsakanin 'Yan Majalisar Wakilai, Ana Zargin APC Na Zawarcin Gwamna

  • An samu sabani tsakanin 'yan majalisar Osun, Bamidele Salam da Oluwole Oke, kan zargin zawarcin Gwamna Ademola Adeleke zuwa APC
  • Salam ya bayyana cewa shugabannin APC ne ke zawarcin Gwamna Adeleke, amma gwamnan ya ki amincewa da tayin barin PDP
  • Oke kuma ya karyata zargin, yana mai cewa Adeleke bai cancanci zawarci daga APC ba, inda ya zargi gwamnan da neman hanyar shiga jam'iyyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osun - An samu takaddama mai zafi tsakanin 'yan majalisar wakilai biyu daga Osun, Bamidele Salam da Oluwole Oke kan gwamnan jihar, Ademola Adeleke.

An ce rigimar ta su ta fara ne kan ikirarin cewa shugabannin jam’iyyar APC na kokarin jan hankalin Gwamna Adeleke da ya fice daga PDP kafin zaben 2026.

Fada ya barke tsakanin 'yan majalisar wakilai daga Osun kan batun komawar Gwamna Adeleke APC
'Yan majalisar wakilai biyu daga jihar Osun, Bamidele Salam da Oluwole Oke a zauren majalisa. Hoto: Mp Oluwole Oke-BOO, Bamidele Salam
Asali: Facebook

An zargi APC da zawarcin gwamnan Osun

Lamarin ya sake daukar hankali ne bayan rahotannin da suka nuna cewa Adeleke ya taba tunanin sauya sheka zuwa APC, amma daga baya ya janye, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Hon. Salam, dan majalisar da ke wakiltar Ede ta Kudu, Ede Arewa, Egbedore da Ejigbo, ya karyata ikirarin a wata wallafa da ya yi a Facebook, inda ya ce shugabannin APC ne ke neman Adeleke ya shigo jam’iyyar.

“Gwamna Adeleke bai taba nuna sha’awar komawa APC ba. A maimakon haka, shugabannin jam’iyyar ne ke rokon sa, kuma kullum yana ce musu a’a,” inji Salam.

An karyara ikirarin dan majalisar Osun

Amma a nasa bangaren, Hon. Oke wanda kwanan nan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, kuma yake wakiltar Obokun/Oriade, ya soki zargin cewa APC na zawarcin Adeleke.

“Ta yaya za a ce shugabannin APC na kasa suna rokon Gwamna Adeleke da ya shigo jam’iyyar? Wannan karya ce da bata da tushe. Haba,” inji Hon. Oke.

Ya kara da cewa:
“Da ni ne Adeleke, da na tattara karfina na kalubalanci gwamnatin da ke mulki kamar yadda Gwamna Aregbesola ya yi a 2014, in fuskanci sakamakon a 2026.
"Ko na ci ko na fadi, to Allah ne kadai ya sani. Gwamna Adeleke dai ya riga ya kafa suna a matsayin gwamnan jihar Osun.”
'Yan majalisa da APC sun tafka magana kan yiwuwar sauya shekar gwamnan jihar Osun
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP. Hoto: @AAdeleke_01
Asali: Instagram

APC ta yi martani kan zawarcin Gwamna Adeleke

Tun da farko, APC ta fitar da wata sanarwa inda ta mayar da martani ga Hon/ Salam, tana mai cewa dan majalisar bai fahimci abubuwan da ke faruwa a jam’iyyarsu ba.

Sanarwar ta ce:

“Za mu iya yafewa Salam saboda jahilcin sa. Matsayin da yake kai na tilasta masa ya yi jawabi don nuna cewa har yanzu yana goyon bayan jam’iyyar da ke yankin sa domin samun tikitin sake tsayawa takara.
“Yaya za a ce jam’iyyar APC da ke da cikakken iko a kan kananan hukumomi a jihar, kuma da ta karbo manyan jiga-jigai daga PDP, tana rokon gwamna maras tsari da ya shigo jam’iyyar? Wannan magana bata da ma’ana.

“Gaskiyar magana ita ce, Adeleke yana cikin rudani da rikicewa. Yana ta yawo daga Osogbo zuwa Abuja, daga can zuwa Lagos, London, Amurka, Canada, Dubai har France yana neman hanyar shigowa APC, amma bai samu nasara ba.”

'Ina nan daram a PDP' - Gwamna Adeleke

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sake tabbatar da cewa yana nan daram a jam’iyyar PDP kuma ba ya shirin sauya sheƙa zuwa APC.

Adeleke ya bayyana haka ne yayin wani taron shugabanni da masu ruwa da tsaki na PDP a jihar Osun, da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Osogbo.

Shugabannin jam’iyyar sun nuna farin ciki da wannan matsayi na gwamnan tare da tabbatar masa da cikakken goyon bayansu domin tazarce a 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »